Yau 24 ga wata da safe, an kammala aikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a birnin Xining da ke lardin Qinghai cikin nasara.
Kafin bikin fara mika wuta da aka shirya a karfe 8 da safe, dukkan mutanen dake halarta bikin sun nuna ta'aziyya ga mutanen da suka rasa rayukansu a bala'in girgizar kasa na gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan har tsaron minti daya.
Shugaban cibiyar nazarin ilmin likitanci na babban tsaunin Qinghai kuma mai nazari a cibiyar nazarin ilmin injiniya ta kasar Sin Wu Tianyi mai shekaru 71 da haihuwa ya zama mutum na farko da ya dauki wutar, kuma ya fara mika wutar a babban fili a birnin Xining, daga wancan lokaci, an fara mika wuta a birnin Xining, bayan da mutane masu mika wutar su 291 suka mika wutar, mutum mai mika wuta na karshe ya konna wutar dake kwanon a gidan baje kolin kayayyakin gargajiya na lardin Qinghai.
Yau 24 ga wata da yamma, za a dauki wutar ta wasannin Olympics na Beijing zuwa birnin Yuncheng dake lardin Shanxi ta hanyar jirgin sama. A ran 25 ga wata, za a cigaba da mika wutar a birnin Yuncheng.(Abubakar)
|