Kabilar Hezhe tana daya daga cikin kananan kabilun kasar Sin 55, kuma har yanzu yawan mutanenta bai kai dubu 5 ba. Mutanen kabilar Hezhe suna zama a yankunan da ke kusa da koguna 3, wato kogin Heilongjiang da kogin Wusuli da na Songhuajiang wadanda suke arewa maso gabashin kasar Sin. Muhimmiyar sana'ar da mutanen kabilar suke yi ita ce kama kifi da farauta. A cikin shirinmu na yau, za mu bayyana muku yadda wani masunci dan kabilar Hezhe yake kama kifi a cikin yini daya a kogin Wusuli.
A wata rana da safe, hazo yana cike kogin Wusuli, ruwan kogin a kwance yake. Kamar yadda ya saba yi a da, You Zhimin da dansa, yan kabilar Hezhe na lardin Heilongjiang sun tuka karamin jirgin ruwa nasu sun fara aikinsu na kama kifi. Sun yi minti misalin 20 bayan tashinsu daga tashar ruwa, sun isa yankin kamun kifi sun hada jirgin ruwa nasu da saraun jiragen ruwa da ke kogin.
Wakilinmu ya tambaye su cewa,"Me ya sa kun hada jiragen ruwa duka"
Sun ba da amsa cewa, "Muna jiran jefa ragar kamun kifi."
Tambayar wakilinmu cewa, "Za ku jefa raga tare?"
Amsa, "A'a, kowane jirgin ruwa zai jefa daya bayan daya. Idan mun jefa tare, kai, za a shiga halin barkatai."
Wadannan masunta 'yan kabilar Hezhe sun riga sun yi shekaru da yawa suna kama kifi a kan kogin Wusuli. Wane irin kifi yake cikin kogin, wace irin hanyar da ya kamata su bi domin kama kfi, za su iya gaya maka filla filla. Har ma You Juntao wanda ya fi karancin shekaru a cikin wadannan masunta ya iya gaya maka kome da kome. You Juntao, da ne na You Minzhi. Amma ya sha bamban da sauran mutanen kabilar Hezhe, ya taba yin zama a cikin birni har na tsawon wasu shekaru. Ya rina gashinsa sai ya zama gashin rawaya. "Ina da shekaru 23 da haihuwa. Yanzu ina yin aikin kama kifi. A lokacin sanyi, sai na yi wasu kayayyakin ado, alal misali, na yi zane-zane na fatan itatuwa. A gidana, tun daga kakana da mahaifina da babana da kuma kawuna, dukkansu suna yin zane-zane na bawon itatuwa. Lokacin da nake da lokacin wasa, sai na yi nazari kan zane-zane na fatan itatuwa."
A lokacin tsakiyar rana, an yi ruwa kadan, kuma an yi duhu. You Minzhi da dansa sun gama ragar farko ta kamun kifi. A tashar ruwa, masu cinikin kifi sun kewaye su sun zabi kifayen da suke so. Ba da dadewa ba You Minzhi ya sayar da dukkan kifayen da ya kama, ya kuma samu kudin Sin yuan fiye da dari 1 a cikin aljihunsa.
Wakilanmu sun ci abincin rana ne a wani gida dan kabilar Hezhe. Suna mai gida shi ne Mr. Sun. An kawata gidansa sosai da kayayyakin da ke nune-nunen al'adun kabilar Hezhe. Mr. Sun yana daya daga cikin mutanen da ke iya yaren Hezhe. Kabilar Hezhe ba ta da kalmomi, tana da yare kawai. Amma ya zuwa yanzu, mutanen da suke iya yaren Hezhe sun yi kadan kwarai. "Ina shekaru 54 da haihuwa. Wasu lokaci na magana da yaren Hezhe. Iyayena dukkansu sun iya yaren Hezhe. Amma domin babu kalma, da alamar ba za a iya gadar wannan yare cikin sauri ba."
Bayan sun ci abinci, ruwan sama ya yi tsanani. Hazo ya bullo a kan kogin Wusuli. Wakilanmu sun shiga jirgin ruwa na kamun kifi na Gao Wen, dan kabilar Hezhe domin ci gaba da aikinsu. Lokacin da jirgin ruwa ya isa gefen tsakiyar kogin, tsoro ya kama wakilanmu. Domin wannan gefen tsakiyar kogin, iyakar kasa ce da ke tsakanin kasar Sin da kasar Rasha. Idan jirgin ruwa ya ratsa wannan iyakar kasa, za a gamu da hadari sosai. Amma Gao Wen yana da imani sosai. "Ka ga wadannan alamun nufin hanyar jirgin ruwa 2, a gefen da ke wajenmu, yankin kasarmu ne. Amma a gefen da ke wajensu, sai yankinsu ne. Na riga na yi shekaru 20 ina kamun kifi a cikin wannan kogi, ba damuwa, ba zan yi kuskure ba."
Da isar wakilanmu a gefen kogin, sun ga Mr. You Minzhi da dansa suna sallame su. A kowace rana, su kan jefa raga har sau 4. Bisa wannan ma'auni, za su gama aikinsu na wannan rana har tsaka-tsakar dare. (Sanusi Chen)
|