
An gama aikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a ran 23 ga wata a gabar tafkin Qinghai, tafki mafi girma dake nesa daga teku na kasar Sin.

An tashi daga gabashin gabar tafkin Qinghai zuwa yammacin gabar tafkin, tsawon hanyar da aka mika wutar a kai ya kai kilomita 6. Kafin bikin fara mika wutar, dukkan mutanen dake halartar bikin sun nuna ta'aziyya ga mutanen da suka rasa rayukansu a bala'in girgizar kasa na gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan har minti daya.


Masu mika wutar 162 sun shiga cikin aikin mika wutar a ran nan.
A ran 23 ga wata da yamma, an kai wutar zuwa birnin Xining. A ran 24 ga wata, za a yi aikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing na tasha ta karshe a birnin Xining.(Lami)
|