Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-23 15:40:11    
Shugaban jam'iyyar MDC da ke adawa da gwamnatin kasar Zimbabwei ya janye daga tsayawa takarar zaben shugaban kasar a zagaye na biyu

cri
Jiya ranar 22 ga wata, Mr. Morgan Tsvangirai, shugaban babbar jam'iyyar adawa ta kasar Zimbabwei, wato MDC, ya sanar janye jiki daga aikin jefa kuri'a na zaben shugaban kasar a zagaye na biyu da za a shirya a ranar 27 ga wata. Bisa dokar zabe ta kasar Zimbabwei, idan 'dan takara daya ya janye jiki daga aikin jefa kuri'a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, to, wani daban zai zama shugaban kasar ba tare da jefa kuri'u ba. Wato ke nan, 'dan takara daga jam'iyyar ZANU-PF wanda ke kan karagar mulkin kasar, kuma shugaban kasar a yanzu Mr. Robert Mugabe zai cigaba da zama shugaban kasar.

A lokacin da za a yi aikin jefa kuri'a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Zimbabwei ba da dadewa ba, muhimman shugabannin jam'iyyar MDC ta kasar sun yi taro a ranar 22 ga wata a birnin Hararre, babban birnin kasar, inda suka tattauna kan ko jam'iyyar za ta cigaba da shiga zabe a zagaye na biyu, ko a'a a halin da ake ciki a yanzu. A wannan rana da yamma kuma, Mr. Tswangirai ya sanar da janyewa daga zaben a gun wani taron manema labaru, inda ya ce, kan halin da ake ciki na kara tsanantar tashe-tashen hankula a kasar Zimbabwei, bai zai yiyu a shirya wani zabe cikin 'yancin kai da adalci ba, masu jefa kuri'a ba za su nuna fatansu ta hanyar jefa kuri'a ba, shi da kansa kuma ba ya son shiga wannan zabe na nuna karfin tuwo. Kazalika kuma ya yi kira ga M.D.D., da kungiyar AU, da SADC?wato southern african development community, da kuma sauran kasashen duniya da su kula da halin da kasar Zimbabwei ke ciki, don hana cigaba da samun tashe-tashen hankula a kasar. Bayan haka kuma, ya bayyana cewa, a ranar 25 ga wata, idan za a kyautatta halin tsaro, to watakila zai canja shawarar da tsaida kuduri, wato zai cigaba da shiga zaben.

Kakakin jam'iyyar ZANU-PF da ke jan ragamar mulki ta kasar Zimbabwei Mr. Patrick Chinamasa ya bayyana cewa, dalilin da ya sa Mr. Tsvangirai ya tsaida kudurin janyewa daga zabe shi ne, domin hana samun hasara a hakika. Kasashen duniya su ma sun mayar da hankulansu sosai kan wannan.

Tun bayan da aka sanar da sakamakon jefa kuri'a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Zimbabwei a watan da ya wuce,, da shelar shirya aikin jefa kuri'a a zagaye na biyu a ranar 27 ga wata, sai aka ta samu tashe-tsashen hankula a kasar Zimbabwei. Masu goyon baya na MDC, da na ZANU-PF sun kai farmaki ga juna, har ma wasu sun mutu ko ji rauni.

Wannan kuma ya jawo hankula daga kasashen duniya. Babban sakataren M.D.D. Ban Ki-Moon ya aika da manzon musamman zuwa kasar Zimbabwei, don yin bincike, da fahimtar halin da ake ciki dangane da gwamnatin kasar ta dauki matakai don hana da kawo karshen tashe-tashen hankula. Kwanan baya kuma, shugaba Thabo Mbeki na kasar Afrika ta kudu, ya kai ziyarar musamman a kasar Zimbabwei, daya bayan daya ya yi shawarwari tare da shugaba Mugabe na kasar a yanzu, da kuma shugaban jam'iyyar da ke adawa da gwamnatin Tsvagirai, inda ya yi fatan bangarorin biyu za su samu jituwa, da yi kira ga masu goyon bayansu da su dakatar da tashe-tashen hankula, da kuma kafa hadaddiyar gwamnati. Amma, yanzu jam'iyyar da ke kan karagar mulkin kasar, da jam'iyyar da ke adawa da gwamnatin kasar ba su iya nuna amincewa ga juna, har ma suna adawa da juna sosai, kan halin da ake ciki a yanzu, da kyar za a iya kafa hadaddiyar gwamnati.