Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-20 21:46:27    
Muhimman wuraren addinai a birnin Beijing suna sa himma domin maraba da baki daga kasashen waje a lokacin wasannin Olympics

cri
Ofishin kula da harkokin waje na yankin addinin Katolika da ke nan birnin Beijing ya gabatar da cewa, a lokacin wasannin Olympics, za a kara yin amfani da harsunan Korea, da Faransa, da Italiya, da kuma Jamusanci wajen yi salla a manyan choci da ke birnin Beijing. Bayan haka kuma, yankin addinin Katolika a birnin Beijing zai shirya masu aikin sa kai da yawansu ya kai 17, don su shiga cibiyar addinai ta kauyen wasannin Olympics a karshen watan Yuli, ta yadda za su gabatar da hidimar addini ga 'yan wasa daga kasashe daban daban.

Bayan haka kuma, a dukkan masallatai 70 da ke birnin Beijing, an zabi guda 12 daga cikinsu, don su zama muhimman masallatai domin musulmi a lokacin wasannin Olympics. Bugu da kari kuma, majalisar musulumi ta birnin Beijing za ta aika da masu aikin sa kai da yawansu ya kai 16 zuwa cibiyar addinai ta wasannin Olympics, don gabatar da hidimomin addini na musamman domin musulmi. (Bilkisu)