Sa'annan Mr. He ya bayyana cewa, mataki na farko shi ne kafa hanyar musamman ta tafiyar motoci cikin sauri domin wasannin Olympics na Beijing ; Mataki na biyu shi ne, bada tabbaci ga shimfida na'urori marasa shinge domin nakasassu ; Mataki na uku shi ne bada tabbaci ga samarda wani kyakkyawan muhalli ga hanyoyin da 'yan wasa za su ratsa.
An labarta cewa, tun kusan shekaru biyar da suka shige, gwamnatin birnin Beijing ta rigaya ta ware makudan kudade da yawansu ya kai kudin Sin wato RMB yuan biliyan dari da goma wajen gyaran fuskar gine-ginen zirga-zirga da sufuri lokacin da take mayar da aikin bunkasa ababen hawa a gaban komai ; Ban da wannan kuma, za a kara shimfida hanyoyin subway guda 7 a nan Beijing gabannin gasar wasannin Olympics ta Beijing a watan Agusta na wannan shekara, kuma tsawon hanyoyin ababen hawa zai kai kusan kilo-mita 200. Abun da ya burge mutane shi ne wani reshen hanyar subway na Beijing zai ratsa ta babban filin wasan motsa jiki na kasar Sin mai siffar gidan tsuntsu da ake kira ' Bird's Nest' da kuma ginin cibiyar ninkaya ta kasar Sin mai siffar ' Tafkin wanka' da ake kira ' Water Cube' a Turance domin bada hidima kai tsaye ga gasar wasannin Olympics.
An kiyasta cewa, a lokacin gasar wasannin Olympics ta Beijing da za a gudanar a watan Agusta, Beijing za ta karbi 'yan wasa da jami'ai da kuma masu kallon wasan da yawansu ya kai 600,000 daga ketare. Daraktan kwamitin kula da zirga-zirga na birnin Beijing Mr. Liu Xiaoming ya furta cewa: ' Mun yi kwaskwarimar wassu hanyoyin ababen hawa na yanzu bisa ajandar gasanni yayin da muke shirin kebe hanyoyin ababen hawa na musamman guda 34 domin bada hidimomin da suka wajaba ga masu kallon wasanni'. ( Sani Wang) 1 2
|