Wakilin hukumar lafiya ta duniya ta WHO a nan kasar Sin Hans Troedsson ya bayyana yau 20 ga wata a nan birnin Beijing cewar, har yanzu ba'a samu rahoto kan barkewar annoba a yankunan da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su na lardin Sichuan ba.
Tun daga ranar 13 zuwa ranar 16 ga wata, kwararrun hukumar WHO masu kula da ayyukan sake farfado da tsarin kiwon lafiya sun gudanar da bincike a lardin Sichuan. Yau 20 ga wata, Hans Troedsson ya bayyanawa kafofin watsa labaru ayyukan da wadanann kwararru suka tafiyar a Sichuan, kuma ya nuna babban yabo ga kyakkyawar halayya ta mutane masu aikin jinya a yankunan da bala'in girgizar kasa ya galabaitar.
Hans Troedsson ya ce, ya ganema idonsa kan mummunar barnar da bala'in girgizar kasa ya kawo, kuma ya ganema idonsa kan cikakkiyar jaruntakar da masu aikin jinya suka nuna.
Bayan faruwar mummunan bala'in girgizar kasa a lardin Sichuan, hukumar WHO ta rika bayar da goyon-baya ga gwamnatin kasar Sin ta hanyoyi daban-daban. Domin biyan bukatun yankunan dake fama da bala'in, WHO ta samar da injunan aikin jinya, da magunguna, da injunan aikin tiyata da dai sauran kayayyaki.(Murtala)
|