Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-20 20:47:22    
Ya kamata a sa ido da binciken dukkanin kayayyaki da kudaden agaji na yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane

cri
Mataimakin sakataren kwamitin ladabtarwa na tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin, kuma shugaban sashen sa ido da binciken kudade da kayayyakin agaji na yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane na gwamnatin tsakiyar kasar Sin He Yong ya bayyana yau 20 ga wata a nan birnin Beijing cewar, ya kamata a sa ido da gudanar da bincike kan dukkan kudade da kayayyakin agaji na yaki da mummunan bala'in girgizar kasa da ceton mutane, domin bada cikakken tabbaci ga yin amfani da kudade da kayayyakin agaji kan yankunan da bala'in girgizar kasa ya galabaitar da mutanen dake fama da bala'in yadda ya kamata.

He Yong ya jagoranci wani taro a ranar, inda ya saurari bayanai daga sassan da abin ya shafa na gwamnatin tsakiyar kasar Sin, da kungiyoyin jama'a, da rukunin gudanar da bincike na musamman na kungiyoyin fararen-hula, kan yadda suka gudanar da aikinsu.

Mr. He ya yi nuni da cewar, ya kamata a rika sa ido da binciken kan ayyukan yin amfani da kayayyaki da kudaden agaji na yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane a duk lokacin da ake gudanar da ayyukan sake farfadowa. Kazalika kuma, kamata ya yi larduna da birane guda 19 wadanda suka samar da agaji ga yankunan dake fama da bala'in girgizar kasa su kafa hukumomin bada jagora, a wani yunkurin inganta ayyukan sa ido da bincika kan yadda za'a yi amfani da kayayyakin agaji da kudaden karo-karo.

He Yong ya kuma jaddada cewar, ya kamata a yanke hukunci mai tsanani kan duk wata aika-aikar da ta sabawa doka ko ka'ida yayin da ake yin amfani da kudade da kayayyakin agaji na yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane.(Murtala)