Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-20 15:21:24    
Waiwaye Adon tafiya(7)

cri

Lubabatu: Masu sauraro, domin fadakar da masu sauraronmu a kan abubuwan da ke faruwa a nahiyar Afirka, a shekarar 1995, gidan rediyon kasar Sin ya kafa ofishinsa a birnin Ikko da ke kasar Nijeriya, tare kuma da aikawa da wakilansa zuwa ofishin. To, ga shi yau na gayyaci wakilinmu da ke aiki a can ofishin, wanda ya koma nan birnin Beijing a kwanan baya, wato Bello, zuwa filinmu na "waiwaye adon tafiya". To, Bello?barka da komowa gida, kuma barka da zuwa filinmu na "waiwaye adon tafiya".

Bello:Barka, sannu!

Lubabatu:To, sannu! Da farko dai, ko za ka gabatar da kanka zuwa ga masu sauraronmu?

Bello:To, madallah, masu sauraronmu, barkanku da war haka. Ni ne Bello, wakilin gidan rediyon kasar Sin da ke Lagos. Yanzu na komo gida na komo nan kasar Sin domin hutu, kuma na dawo wannan studio, da ma ina aiki a ciki, kuma ina farin ciki sosai, yanzu ina nan ina gai da ku, ina fatan Allah ya kawo muku alheri.

Lubabatu:Dazun nan ka ce, ka koma ne domin ka dan huta kadan, to, shin yaushe ne ka fara aiki a sashen Hausa?

Bello:To, na fara aiki a nan sashen Hausa na CRI kamar shekaru hudu da suka wuce, a shekarar 2004.

Lubabatu:Watakila masu sauraronmu na sha'awar a ina ne ka koyi harshen Hausa?

Bello:Na koyi harshen Hausa ne a jami'ar koyon harsunan waje ta Beijing, tun daga shekarar 2000 zuwa ta 2004.

Lubabatu:wato ka fara aiki a nan sashen Hausa ne bayan ka gama karatu a jami'ar?

Bello:kwarai kuwa.

Lubabatu:Shin yaushe ne ka fara aiki a ofishinmu da ke can birnin Ikko?

Bello:Kamar yadda na fada, na fara aiki a sashen Hausa na rediyon kasar Sin a shekarar 2004, daga baya, kusan bayan shekaru biyu, wato a shekarar 2006, na je Nijeriya, na fara aiki a ofishinmu da ke Lagos.

Lubabatu:watakila masu sauraronmu na sha'awar yadda ofishin ke gudanar da aiki?

Bello:To, yanzu ya kasance da mutane biyu cikin ofishin, akwai ni da abokin aikina, Mr.Wei Xiangnan, shi ya zo daga sashen Turanci na rediyonmu. Aikin da muke yi can birnin Ikko shi ne mu mai da hankali a kan abubuwan da ke faruwa a yammacin Afirka gaba daya, kan fannoni daban daban, kamar su siyasa da al'adu da tattalin arziki da dai sauransu. Kome abin da ya faru, sai mu rubuta labari, edita na rediyonmu za su wallafa labarin. Hanyoyin da muke bi wajen samun labarai sun hada da mu je intabiyu da kanmu fuska da fuska, ko kuma ta tarho, da kuma ta kamfanin dillancin labaru da jaridu daban daban na kasashen Afirka. Domin wannan intabiyu ne, kullum muna yawo cikin nahiyar Afirka, na taba ziyartar Togo da kasar Benin, da Ghana, abokin aikina shi ma ya koma daga birnin Accra kwanakin da suka wuce. Abin da muke yi a Lagos ke nan, wato mu yi yawo mu duba mu yi hira da mutane, mu rubuta, shi ke nan.

Lubabatu:To, tun da kullum kuna ziyara a kasashe daban daban na Afirka, don samo mana labarai da dumi-duminsu, to, shin wadanne muhimman al'amura ka taba ba da rahotanni a kansu?

Bello:Lokacin da nake can Nijeriya, na ga muhimman al'amura da yawa da idona, al'amuran sun hada da babban zaben da aka yi a Nijeriya a shekarar 2007 da bikin rantsar da shugaba Umaru Musa 'Yar Addu'a, da ziyarar sada zumunta da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya kai wa kasar Nijeriya, da babban taron shugabannin kasashen Afirka da na Latin Amurka da aka yi a Abuja, da taron koli na AU da aka yi a Ghana, da dai sauransu. Amma ba wai wadannan al'amuran da ke da muhimman mutane kawai muke mai da hankali a kai ba, har ma muna mai da hankali a kan zaman mutane, kome abin da ya faru a gaban jama'a, kamar yadda ayyukan kasuwanci da aka yi a birnin Ikko, da halin tsaro da tasowar farashin abinci da man fetur da aikin ilmi da aikin kulawa da jama'a da dai sauransu, dukansu muna da sha'awa a kansu, kuma mun rubuta labarai a kansu.

Lubabatu:To, mun gode, kullum a nan sashen Hausa mu kan sami labaran da kuka turo mana daga birnin Ikko, kuma mun gode da irin kokarin da kuka yi.

To, a cikin shekaru biyu da kake aiki a Nijeriya, me ka fi karuwa da shi?

Bello:To, abin da na karu shi ne, na sami abokai da yawa a can, kamar su malam Salisu Dawanau, tsohon mai sauraronmu, kullum muna gai da juna, da na je Abuja, dole ne za mu gamu da juna, mu yi hira.Watan jiya, da na je Abuja, ya zo gamu da ni, kuma ya kawo ruler, ya auna mana tsayin jiki, ya ce za a sa wajen talor, a yi mana riga, wannan ya ba ni mamaki da farin ciki. Da malam Bello Abudullahi, dan wasan kwallon kafa, da ke Lagos, kullum yana kawo mana ziyara, da malam Mohammed Idi Gargajiga, shugaban kungiyar masu sauraronmu da ke Gombe, shi ma ya kawo mana tambayoyi da yawa, har ban yi masa amsa ba tukuna, da Mr Tunde Ikirani, babban darekta na fim, da malam Uwais Idris, da malam Yunusa Alhassan, P.R.O.na masu sauraron rediyo, da malam Baji na Freedom Radio, da malam Yunusa da ke aiki cikin ofishin jakadancin Nijer da ke Abuja, wanda ya iya Sinanci sosai.

Gaskiya ne a cikin wadannan shekaru, na sami abokai na gaskiya da yawa a can Nijeriya, wannan ma abu ne da na fi farin ciki da alfahari da shi.

Lubabatu:Gaskiya na ga ka kulla zumunci sosai da mutanen wurin.

Bello:Ko shakka babu.

Lubabatu:To, yanzu shekaru kusan hudu ke nan kana aiki a nan sashen Hausa, to, idan ka waiwayi wadannan shekaru hudu, yaya aiki a sashen Hausa ke ma'ana a gare ka?

Bello:Na shiga gidan rediyon CRI a shekarar 2004, yanzu shekaru hudu ke nan, da nake maimaita wadannan shekaru da suka wuce, ma iya cewa, na zabi aiki mai kyau, domin ya ba ni damar ci gaba a kan hanyar da na zaba yayin da nake cikin jami'a. A cikin jami'a, na zabi Afirka, na zabi harshen Hausa, na fara fahimta cewa, a can nahiyar Afirka, a can wuri mai nisa, ya kasance da dogon tarihi, da al'adu masu ban sha'awa, da mutane masu zafin nama, da kauna da kirki, da na shiga CRI, shiga cikin sashen Hausa, na fara ganin cewa, wadannan al'adu da jama'a ba su da nisa, ba wai cikin littafi kawai ne ake samu ba, a'a, suna kusa, suna sauraronmu, suna rubuta mana wasiku, suna aiko mana Email, suna buga mana waya, suna tare da mu a ko da yaushe, shi ne dalilin da ya sa na ce wannan aiki ya ba ni damar in ci gaba a kan hanyar da na zaba, in zo kusa da jama'ar Afirka, da al'adunsu masu kyau, masu ban sha'awa. Ban da wannan kuma, mu manema labarai kamar jakada ne, muna gabatar da labaru da al'adun kasashen Afirka ga jama'ar Sin, kuma muna sanar da mutanen Afirka a kan yadda kasar Sin take yanzu, domin bangarorin biyu su fahimci juna, su kulla zumunci da abokantaka.

Lubabatu: To, gaskiya, aikin da muke yi aiki ne mai ma'ana sosai, kuma ni ma ina alfahari da wannan aikin da muke yi. To, a ran 1 ga watan Yuni na shekarar da muke ciki, sashen Hausa na rediyon kasar Sin ya cika shekaru 45 da kafuwa, to, a daidai wannan lokaci, ko kana da abin da kake son fada?

Bello:Abin da nake so in fada shi ne, "na gode". Cikin wadannan shekaru 45 da suka wuce, masu sauraronmu da ke kasashe daban daban suna kaunarmu, suna mana goyon baya sosai, shi ya sa a lokacin da ake bikin ranar haihuwar sashen Hausa namu, ina so in nuna godiya ga masu sauraronmu, abokanmu na gaskiya. Ban da wannan kuma, ina son gai da abokaina da ke can Nijeriya, ina fatan Allah ya ba su zaman lafiya, da kwanciyar hankali da alheri.

Lubabatu:To, da fatan su ji.

To, masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau, amma kada ku manta, a makon gobe war haka, za mu ci gaba da kawo muku shirye-shiryenmu na "waiwaye adon tafiya", da haka ni Lubabatu daga nan Beijing ke cewa, "sai Allah ya kai mu ranar Jumma'a mai zuwa. (Lubabatu)