Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-20 10:58:20    
Sin na iyakacin kokarin bada tabbaci ga samun kyawawan zirga-zirga a lokacin gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Ko kuna sane da cewa, ana samun karuwar yawan motoci a 'yan shekarun baya a nan birnin Beijing. Hakan ya kawo babban matsi ga zirga-zirga. Da yake gasar wasannin Olympics ta Beijing na karatowa, shi ya sa mutanen ciki da wajen kasar suka fi mai da hankali kan cewa shin ko sassan kula da harkokin zirga-zirga na birnin Beijing za su iya cimma bukatun zirga-zirga lokacin da ake gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing. Game da wannan dai, mai magana da yawun ma'aikatar zirga-zirga da sufuri ta kasar Sin Mr. He Jianzhong ya bayyana jiya Alhamis a nan Beijing, cewa ma'aikatar za ta dauki jerin matakai masu amfani don bada tabbaci ga samun kyawawan zirga-zirga a lokacin wasannin Olympics na Beijing.

Bisa kididdigar da aka yi an ce, yanzu birnin Beijing na da kimanin mutane miliyan goma sha biyar; kuma yawan motoci da birnin yake da su a halin yanzu ya karu zuwa sama da miliyan uku daga miliyan daya yau da shekaru 10 da suka gabata ; Kazalika, yanzu ana samun karin motoci dubu daya a kowace rana. Hakan ya janyo babban matsi ga zirga-zirgar motoci a nan birnin Beijing. Mr. He Jianzhong ya furta cewa : ' Sassan da abin ya shafa na birnin Beijing za su dauki jarin matakai masu amfani don gudanar da zirga-zirgar mototi kamar yadda ya kamata a lokacin da ake gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing.'


1 2