Ran 19 ga wata, Mr. Girma shugaban kasar Ethiopia ya ce, bayan bala'in girgizar kasa da ya auku a ran 12 ga watan Mayu a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin, gwamnati da shugabannin kasar Sin sun dauki ingantaccen matakai cikin gaugawa, wannan ya sami yabawo sosai daga kasashen duniya.
Mr. Girma yi wannan nuni yayin da yake karbar takardar nadi da Mr. Gu Xiaojie sabon jakadan kasar Sin da ke kasar Ethiopia ya gabata, ya yi maraba da Mr. Gu Xiaojie, kuma ya sake jajantawa gwamnati da jamar kasar Sin bisa ga bala'in girgizar kasa da ya auku, kuma ya yi nuni da cewa, kasar Ethiopia tana mai da hankali sosai wajen bunkasa huldar da ke tsakaninta da kasar Sin, tana son yin kokari tare da kasar Sin domin bunkasa huldar da ke tsakaninsu.
|