Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-19 21:17:06    
Wu Bangguo ya ce, kasar Sin ta samu babbar nasara ta wannan wa'adi wajen yaki da babbar girgizar kasa da gudanar da aikin ceto

cri

Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mr. Wu Bangguo ya bayyana a ran 19 ga wata a birnin Beijing cewa, a halin yanzu, kasar Sin ta riga ta fara gudanar da aikin samar da kayayyaki don ceto da aikin sake gina gidaje a yankunan girgizar kasa na gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, a halin yanzu dai, jama'ar da ke yankunan suna zaman rayuwa mai inganci, sun kwantar da hankulansu, muna iya ganin cewa, kasar Sin ta samu babbar nasara ta wannan wa'adi wajen yaki da babbar girgizar kasa da gudanar da aikin ceto.

Mr. Wu ya yi wannan bayani ne a gun taro na karo na biyar kan raya dangantakar abokantaka tsakanin majalisun dokokin kasashen Asiya da Turai.

Ban da wannan kuma, mu sami wani labari cewa, kakakin ma'aikatar sadarwa da sufuri ta kasar Sin Mr. He Jianzhong ya bayyana a ran 19 ga wata a birnin Beijing cewa, ma'aikatar tana shirin maido da dukkan hanyoyin mota da suka lalata sakamakon babbar girgizar kasar cikin shekaru 3 masu zuwa.(Danladi)