Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-19 17:28:07    
An bude taron abokantaka na majalisun Asiya da na Turai a karo na biyar a birnin Beijing

cri
Yau Alhamis da safe, a nan birnin Beijing, an bude taron abokantaka na majalisun Asiya da na Turai a karo na biyar. Mr Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya halarci bikin bude taro, kuma ya bayar da jawabi a kan babban jigon taron. A cikin jawabinsa, Mr Wu ya bayyana halin da ake ciki a kasar Sin dangane da aikin yaki da bala'in girgizar kasa da ceton jama'a ga shugabannin majalisun da wakilansu na kasashen Asiya da na Turai daban daban, kuma ya gabatar wa taron da shawarwari kan batun samun bunkasuwa a nan gaba.

Za a shafe kwanaki uku ana yin wannan taro, babban jigon taron shi ne "inganta hadin gwiwa a tsakanin Asiya da Turai, don sa kaimi ga samun bunkasuwa tare". A gun bikin bude taron, Mr Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya amince da wannan babban jigon taron. Ya ce, "inganta hadin gwiwa a tsakanin Asiya da Turai don sa kaimi ga samun bunkasuwa tare", batu ne da ke jawo hankulan dukan jama'ar kasashen Asiya da na Turai. Bisa wannan babban jigo, taronmu zai binciki rawar da ake takawa ta hanyar hadin gwiwar majalisu kamar yadda ya kamata. Wannan ya dace da zamanin yanzu da burin jama'ar dukan kasashen Asiya da na Turai, kuma yana da muhimmanci sosai ga kara fahimtar juna, da sa kaimi ga hadin gwiwa bisa halin da ake ciki, da sa kaimi ga samun wadata tare.

Bayan haka Mr Wu Bangguo ya gabatar wa taron shawarwari a kan batun samun bunkasuwa a nan gaba. Ya ce, "ya kamata, a yi la'akari da manyan abubuwan da ke jawo kasashe mambobi daban daban, a yi tattaunawa cikin sahihanci, a yi hakuri da ma'amala da juna, kuma bisa ka'idojin yin shawarwari cikin daidaici da neman samun ra'ayoyi iri daya ba tare da yin la'akari da abubuwa da aka sha banban a kansu ba, a kawar da banbancin ra'ayoyi kamar yadda ya kamata, a yi dukan abubuwa da ake iya yi don samun ra'ayoyi ba su daya, a yi ta neman samun ra'ayoyi ba su daya don moriyar juna. Ya kamata, a kara kokari wajen sa kaimi ga yin ma'amalar al'adu a tsakanin Asiya da Turai, a kara fahimtar juna a fannin tarihi da al'adun gargajiya, a kara dankon aminci da amincewa a tsakanin jama'a, a yi ta inganta hadin gwiwa bisa burin jama'a da ra'ayoyin zamantakewar al'umma."

A cikin jawabinsa, Mr Wu Bangguo ya kuma yi dogon bayani don bayyana abubuwa a kan yadda ake yaki da bala'in girgizar kasa don ceton jama'a a kasar Sin.

Tun bayan da mummunar girgizar kasa ta auku a kasar Sin, bi da bi kasashe daban daban sun bai wa kasar Sin taimako, sun nuna tsayayyen goyon baya ga ayyukan da kasar Sin ke yi wajen yaki da bala'in girgizar kasa don ceton jama'a. A gun bikin bude taron, a madadin gwamnatin kasar Sin da jama'arta, Mr Wu Bangguo ya nuna godiya ga gamayyar kasa da kasa. Ya ce, "a nan, ina so in jaddada sosai cewa, yayin da take yaki da bala'in girgizar kasa don ceton jama'a a wannan gami, kasar Sin ta sami babban goyon baya da taimako daga wajen gwamantocin kasashe daban daban da jama'arsu ciki har da kasashen Asiya da na Turai. Kungiyoyin ba da agaji da kungiyoyin likitoci na kasashe da dama sun kuma yi aikin yaki da bala'in girgizar kasa don ceton jama'a tare da jama'ar kasar Sin. Sosai da sosai, wannan ya gwada babban zumuncin da jama'ar kasashen duniya daban daban ke nuna wa jama'ar kasar Sin. A nan, a madain gwamnatin kasar Sin da jama'arta, kuma da zuciya daya na sake nuna godiya ga gamayyar kasa da kasa. (Halilu)