Ran 18 ga wata, Mr. Seyoum ministan harkokin waje na kasar Ethiopia ya ce, bayan bala'in girgizar kasa da ya auku a ran 12 ga watan Mayu a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin, gwamnati da shugabannin kasar Sin sun dauki matakai cikin gaugawa, kuma matakan da suka dauka sun sami kyakkyawan sakamako sosai.
Yayin da Mr. Seyoum ke ganawa da Mr. Gu Xiaojie sabon jakadan kasar Sin da ke kasar Ethiopia, ya sake jajantawa gwamnati da jamar kasar Sin bisa ga bala'in girgizar kasa da ya auku, kuma ya yabawa kokarin da gwamnatin kasar Sin ta yi. Mr. Seyoum ya ce, bayan da wannan matsanancin bala'in ya faru, gwamnatin kasar Sin ta dauki ingantattun matakan ceto cikin gaugawa, wannan ya zama abin koyi wajen tinkarar bala'in halittu, kuma wannan ya nuna babban karfin gwamnatin kasar Sin. Kasar Ethiopia da sauran kasashe masu aminci suna jin farin ciki sosai.
Mr. Gu Xiaojie ya ce, bayan bala'in girgizar kasa ya faru, shugabannin kasar Ethiopia sun aika da wasikun jaye ga kasar Sin, wanan ya nuna goyon bayan da bangaren kasar Ethiopia ke baiwa kasar Sin, kasar Sin ta yi godiya kan wannan.
|