Bayan da kasar Sin ta ci gaba da gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, lardunan dake cikinta masu nesa da teku su ma sun samu ci gaba. Wasu manyan masana'antun dake bakin teku sun yi kaura zuwa wadanan larduna,birnin anchang,babban birni na lardin Jiangxi sun yi maraba da zuwan 'yan kasuwa na gida da na waje sabo da yanayinsa na zuba jari ya inganta. Musamman bayan da shekara ta 2006 da mujallar mako mako ta Amurka da ake kira News a turance ta daukaka birnin Nanchang a kan matsayi na daya daga cikin manyan birane goma aduniya da suka jawo hankulan mutanen duniya, bakin da ke zuwa birnin domin karo ilimi da ciniki da kuma aiki sai kara yawa su ke yi.
Mr H.Kulkarni dan kasar Indiya ne, gidansa yana cikin unguwar Qianxiyuan a birnin Nanchang, ba iyalinsa daya kawai ba da akwai sauran iyalai guda bakwai na kasar Indiya sun zauna cikin wani gini na unguwar dake cikin birnin Nanchang wanda ya sha banban da na saura. Dukkansu manyan ma'aikata ne na wani kamfanin kera motocin noma mai suna Mahengda na kasar Sin. Saboda haka ana kiran ginin nan ginin sada zumuncin da ke tsakanin Sin da Indiya.
Mr.H.Kulkarni yana da shekaru 38 da haihuwa a wannan shekarar da muke ciki. Ya zo birnin Nanchang ne daga birnin Bombay,babban birni na farko a kasar Indiya a shekara ta 2005.A ganinsa Idan an kwatanta birnin Nanchang da birane Beijing da Shanghai,birnin Nanchang bai kai wadannan biranen ba ko yawan mutane ko bunkasuwa, duk da haka birnin Nanchang yana da nasa abin ban sha'awa. Ya ce,
"Da ya ke birnin Nanchang bai kai girman birnin Shanghai da birnin Beijing ba,Nanchang birni ne da ya fi dacewa da yin zama a ciki, dalili kuwa shi ne kana da lokaci mai tsawo na yin zama tare da iyalinka. Muna jin dadin zama a wannan birnin in na samuwasu matsaloli, aminan dake cikin unguwa za su iya ba da taimako."
Mr. H Kulkarni ya fi ba da fiffiko ga iyali, da farkon farko ya zo kasar Sin ne shi kansa.Ya gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa abin da ya ganam idonsa a filin jiragen sama ya burge sa. Ya ce,
"A ganina mutnen kasar Sin suna da kirki sosai,suna so su ba da taimako ga baki. Da na sauka a kasar Sin ba na ji sinanci, mutanen Sin sun ba ni taimako. Alal misali a filin jiragen sama a gaban teburin karbar baki, idan ba ka iya magana da turanci, mutanen Sin su kan yi iyakacin kokarinsu na ba ka taimako. Ina so in kulla aminci da Sinawa."
A shekara ta 2006 ne Mr Hkulkarni ya kawo matarsa da dansa a birnin Nanchang, daga nan iyalinsa ya fara wani sabon zama. A cikin wannan shekara, karo na farko ne da birnin Nanchang ya buga taswira da sinanci da turanci a hade, a cikin taswirar birnin Nanchang, dukkan wurare masu kyaun gani da unguwoyi suna da sunayensu na turanci, haka kuma kamfanoni da manyan makarantu da hukumomin gwamnati.
Matar Mr H.Kulkarni tana suna na sinawa wato Li Yue. Tana aiki a wani kamfani na kasar Britaniya a birnin Nanchang. Ko wane lahadi ita da mijinta Kulkarni sun je jami'ar Nanchang domin koyon sinanci. In ta samu sarari ta kan je titin ciniki. A cikin 'yan shekarun baya manyan kamfanoni na duniya kamar su Wal-mart da KFC da Man donalds sun bude sassansu a birnin Nanchang, lalle masaye sun samu sauki wajen saye kayayyakin da suke so.
Ta ce"birnin Nanchang yana da kyaun gani sosai, ya fi dacewa da yin zama a ciki, an kuma kayatar da birnin da ciyayi da bishiyoyi da furanni, kuma birni ne mai faranta rai. Muna dafa abinci a gida wani lokaci na kan je babbar kasuwa in saye ganyayen ci. Ina jin sinanci kadan babu babbar matsala wajen yin mu'amala da mutanen wuri."
Ga matar H Kulkarni abin da ta fi so shi ne yawo cikin kasuwa, Da ta samu dama ta kan je kasuwar Wanshougong dake cikin birnin Nanchang domin saye abubuwa.Ta yi magana da sinanci,wani sa'i ma ta nemi rangwame daga dan kasuwa, wannan abu ya ba ta sha'awa sosai. Mutanen lardin Jiangxi sun fi ci abinci mai zafi, masu yawon bude ido da yawa ba su saba da abincinsu ba,amma wannan ba matsala ba ce ga iyalin Mr H.Kulkarni.
Ta ce" wasu abinci na birnin Nanchang na da zafi sosai,wannan ba matsala ba ce ga mutanen Indiya, haka ma abincin soya. Yanzu mun saba da abincin sinawa. Wani lokaci mun je manyan dakunan sayar da abinci domin cin abinci, muna fara koyon sinanci, muna iya yin mu'amala cikin sinanci a saukake."
A gida Mr H kulkarni uba ne nagari, kuma miji ne mai kirki. A cikin kamfani shi jagora ne mafi nagarta. Wani ma'aikaci mai suna Xue Wenkong wanda ya taba aiki tare da Mr Kulkarni ya gaya wa wakilin gidan rediyonmu ta hanyar tarho cewa har abada ba zai manta da lokutan da yake aiki tare da Mr Kulkarni ba.
Ya ce"shi manaja ne na farko gare ni, ya ba ni tasiri mai yawan gaske, shi kuma dattijo ne da ya cancanci a girmama shi, shi kuma babban aminina ne a cikin zaman yau da kullum."
Da ya tabo batun kamfaninsa na Mahengda, Mr H.Kulkarni ya yi alfahari da cewa, "Mutanen Indiya da mutanen Sin suna da abubuwa da yawa na makamanci. Indiya ta fi yawan mutane a duniya, kuma tana da dadadden tarihi, kasar Sin tsohuwar kasa ce mai wayin kai. Kasar Sin da Indiya manyan kasashe ne na noma, babu shakka kamfanin Mahengda zai iya samun nasara a kasar Sin."
Dan Mr Kulkarni yana da suna daya da wani shahararen dan wasan dambe na kasar Sin wato Li Xiaolong wanda kuka fi sani da suna Bruce Li, ya fi ubansa dadewa wajen mu'amala da kasar Sin. Kafin ya zo nan kasar Sin ya yi shekaru biyar ya koyi wasan Wushu makamancin wasan Gongfu na kasar Sin. Wani malamin koyarwa na wasan ya ba shi wannan suna, a bayyane wannan malamin ya yi fatan Dan Kulkarni ya zama wani kwarraren dan wasan Wushu. Ga shi a yau Li Xiaolong yana karatu a wata makaranta dake amfani da sinanci da turanci. Bayan aji ya kan yi wasani na kwallon kwando da kwallon kafa da kuma wasan Wushu. A cikin shekara daya da 'yan kai,ya koyi sinanci yanzu ya iya magana da sinanci na saukakke, ya saje da kansa da 'yan makaranta sosai. Ya ce" mutanen wurin suna da kirki kwarai da gaske, wani lokaci su kan koya mini sinanci, da na kasa gane abin da ake nufi, su kan gwada mini wasu hotuna ko abubuwa na zahiri. Bisa taimakonsu, yanzu na iya magana da sinanci a saukakke, na kuma sami aminai sinawa da yawa."
Mr H.Kulkarni da iyalinsa suna zaman jin dadi a kasar Sin.Bayan shekaru biyu wa'adin kwangilarsa zai cika,za su koma gida a kasar Indiya, duk da haka Mr Kulkarni ya ce har abada ba zai mantar da zamansa a kasar Sin ba,abin tunaniya ne a duk rayuwarsa. Yayin da wakilin gidan rediyo na kasar Sin ya tashi daga gidansa,dan Mr Kulkarni Li Xiaolong ya yi magana da daidaitaccen sinanci inda ya bayyana abin dake cikin zuciyarsa cewa. "ina kaunar kasar Sin."
Jama'a masu sauraro,kun dai saurari wani bayanin da wakilin gidan rediyonmu ya rubuto mana kan wani dan kasar Indiya da iyalinsa a kasar Sin.
Yanzu za mu karanta wani gajeren bayanin da aka buga a cikin jaridar People's daily kwanan baya cewa samar da ilimi a gida tun tuni yana da muhimmanci. Bisa wani binciken jin ra'ayoyin jama'a da Hadaddiyar kungiyar mata ta kasar Sin ta yi a makon jiya, an ce a ganin yawancin iyayen iyalai, a fara samar da ilimi a gida tun tuni yana da muhimmacin gaske. Kashi 89 bisa dari na iyayen da aka ji ra'ayoyinsu kan tarbiyyar yara suna masu ra'ayin cewa koyar da yara a gida yana da muhimmanci ga makoman yara .Ba mazauna birane kawai suke da wannan ra'ayi ba har kama manoma a karkara su ma suna rike da wannan ra'ayi a kasar Sin. Bisa al'adun gargajiya na kasar Sin, ana renon yara ne domin iyaye su sami madogara yayin da suka tsufa. Amma yayi ya canza. Iyaye masu yawan gaske sun sa lura kan makomar yaransu, sun fi so 'ya'yansu su samu guraban aiki masu sauki da albashi mai tsoka da kuma za su taka muhimmiyar rawa a cikin zamantakewa.Tare da ci gaban da kasar Sin ta samu wajen harkokin tsaro, iyaye da dama ba su nuna damuwarsu yayin da suka tsufa. Ko ma a karkara, wasu kanana hukumomi na kasar Sin sun fara kafa sassan kula da tsofafin manoma ta hanyar ba da kudin fensho. Duk da haka kasar Sin ba ta kai matsayin kasashen yamma wajen bunkasa masana'antu ba, tana ci gaba da kokarinta wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.(Ali)
|