Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-18 21:12:04    
Jama'ar lardin Sichuan na kasar Sin na rubanya kokari wajen yin aikin samar da kayayyaki don ceton kansu

cri
Yayin da ake zurfafa ayyukan yaki da bala'in girgizar kasa da ceton jama'a, jama'ar wuraren lardin Sichuan da bala'in ya shafa suna nan suna rubanya kokari wajen yin aikin samar da kayayyaki da ceton jama'a, ta yadda za su sake gina wurarensu. A fannin aikin masana'antu, sun riga sun tsara jadawalin farfado da aikin samar da kayayyaki, a fannin aikin noma kuma, suna bin hanyoyi daban daban wajen noman amfanin gona da girbe su cikin sauri. A gundumomin lardin Sichuan da bala'in ya galabaita sosai, jama'a suna aikin wurjanjan a ko ina don ceton kansu da sake raya wurarensu.

Kafin aukuwar girgizar kasa, tattalin arzikin lardin Sichuan ya kai matsayi na 8 a dukan kasar Sin. Mummunan bala'in girgizar kasa ya kawo wa lardin Sichuan babbar hasara. Yanzu, yayin da ake yaki da bala'in da ceton jama'a, kuma ana rubayan kokari wajen farfado da aikin samar da kayayyaki. Malam Liu Qibao, sakataren kwamitin Jam'iyyar Kwaminis ta Sin a lardin Sichuan ya bayyana cewa, "wajibi ne, mu yi aikin tukuru, mu dogara da karfin kanmu, mu kawar da tunani iri na dogara da taimako. Kuma mu nuna karfin zuciya wajen ceton kanmu. A wurarenmu da bala'in ya shafa, kamata ya yi, mu yi haka ta yadda za mu dogara da karfinsu wajen sake raya sabbin wurarenmu masu kyau iri na gurguzu."

Aikin masana'antu ya taba zama sana'ar ginshikin tattalin arzikin lardin Sichuan, kuma ya sha hasara mai tsanani a cikin bala'in girgizar kasa. Birnin Chengdu, fadar gwamnatin lardin Sichuan ya dauki kashi 1 cikin kashi 3 na tattalin arzikin lardin Sichuan. Malam Li Chuncheng, sakataren kwamitin Jam'iyyar Kwaminis ta Sin a birnin ya ce, "ya kamata, mu mai da hankali sosai ga tasirin da bala'in girgizar kasar ke kawo wa bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma a birnin Chengdu yanzu kuma nan da wani dogon lokaci. Hasarar da ya kawo ya yi yawa, don haka aikin sake gina wurarenmu yana da wahala. A cikin irin wannan hali ne, bayan girgizar kasa, mun iya farfado da aikin samar da kayayyaki tun da wuri, mun tsara manufofi da matakan da za a dauka don kara bunkasa tattalin arziki cikin dogon lokaci daga dukkan fannoni. Tabbas ne, za mu iya farfado da tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al'umma a birnin Chengdu cikin wani lokaci mafi kankani."

Yanzu, manyan masana'antu na birnin Chengdu wadanda suka riga suka farfado da aikinsu ya kai 3285, sun dauki kashi 95 cikin dari bisa dukkan masana'antu na birnin. Bisa jadawalin da lardin ya tsara, nan da watanni uku za a ba da taimako ga sauran masana'antu wajen farfado da aikinsu.

A fannin aikin noma, yanzu muhimmin lokaci ne da ake yin aikin gona, kuma an riga an shiga lokacin girben hatsi da tsire-tsiren man girke a wuraren da bala'in ya shafa. Sojoji da masu aikin sa kai wadanda ke aikin wurjanjan don yaki da bala'I da ceton jama'a suna aiki tare da manoma wajen yin shuke-shuke da girbi a wuraren da bala'in ya shafa.

A kauye mai suna Badi na gundumar Shehong ta lardin Sichuan, manomi Zhang Qiulin yana shan aikin shuke-shuke a cikin gonakinsa. Ko da yake gidajensa sun rushe a sakamakon girgizar kasa, amma bisa taimakon da gwamnati ta bayar, shi da iyalinsa suna kwana cikin tanki da aka kafa cikin gajeren lokaci, yana cike da imani ga farfado da aiki da sake gina wurinsa. Ya ce, "bai kamata mu jira gwamnatin da ta ba mu taimako wajen yin kome ba, kamta ya yi, mu dogara da karfinmu, wajen yin aikin samar da kayayyaki don ceton kanmu. Mu manoma muna nan tare da gonakinmu, idan mun yi kokari tare, to, za mu kawar da dukan wahalhalun da muke fuskanta, ta haka zamu ji dadin zamanmu a nan gaba." (Halilu)