Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-18 20:42:29    
Gwamnatin kasar Sin za ta kara nuna goyon baya ga aikin sake gina gidaje bayan faruwar girgirzar kasa

cri

A ran 18 ga wata, firayin ministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao ya shugabanci taron din din din na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, inda aka yanke shawara cewa, kasar Sin za ta kara nuna goyon baya ga aikin sake gina gidaje bayan faruwar girgizar kasa a gundumar Wenchuan a fannonin kudi, da haraji, da filayen kasa, da samun ayyukan yi, da kuma sayen hatsi daga wurin.

Taron ya ce, za a kaddamar da asusun kudi na gwamnatin tsakiya wajen sake gina gidaje. Ban da wannan kuma, taron ya yanke shawara cewa, za a mayar da jama'ar da suka gamu da matsala sakamkon girgizar kasa a cikin tsarin ba da agaji na neman ayyukan yi.

Ban da wannan kuma, taron ya bukaci hukumomin kwamitin tsakiya na jam'iyya da na gwamnatin kasa da su taka wata muhimmiyar rawa wajen tsimin makamashi da rage yawan gurbataccen hayaki da ake fitarwa, da kuma kafa wata al'umma mai tsimin makamashi.(Danladi)