Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-18 19:19:01    
Kasar Sin za ta samu bunkasuwar tattalin arziki kamar yadda ya kamata bayan wasannin Olympics na Beijing

cri
A gun taron dandalin tattaunawa kan tattalin arziki na wasannin Olympics na shekarar 2008 da aka shirya a jiya 17 ga wata a nan birnin Beijing, daya bayan daya jami'ai, da masana daga gida da waje suka bayyana cewa, kasar Sin za ta samu bunkasuwar tattalin arziki bayan wasannin Olympics.

Masanin tattalin arziki, kuma babban sakataren asusun nazarin gyare-gyaren tsarin tattalin arziki na kasar Sin Mr. Fan Gang, yana ganin cewa, kara karuwar tattalin arziki da kasar Sin za ta samu na dogara kan taimakon da wasannin Olympics zai bayar, wasannin Olympics zai sanya kasar Sin ta kara shiga kasuwar duniya kamar yadda ya kamata, kuma zai kara kyautata ingancin tsarin tattalin arziki, da ra'ayoyin jama'a.

Shugaban kwamitin kasuwa na hukumar wasannin Olympics ta duniya Heiberg ya ce, wasannin Olympics ya sanya birnin Beijing zai zama wani birni bisa matsayin duniya, haka kuma kasar Sin na kara jawo hankula daga kasashen duniya. (Bilkisu)