
Ran 18 ga wata da safe da misalin karfe 9 da rabi, an fara mika wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Kashi na jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin.


Birnin Kashi, zango ne na biyu a kan hanyar mika wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a jihar Xinjiang. Masu rike da wutar 208 za su mika wa juna wutar a kan hanya mai tsawon misalin kilomita 6.5.(Tasallah)
|