Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-17 20:42:36    
Za'a yi aiki tukuru wajen bada tabbaci ga ayyukan jinya da kiwon lafiya na gasar wasannin Olympics, in ji ministan kiwon lafiya na Sin

cri
Ministan harkokin kiwon lafiya na kasar Sin Chen Zhu ya bayyana yau 17 ga wata a nan birnin Beijing cewar, za'a dukufa ka'in da na'in wajen bada tabbaci ga ayyukan jinya da kiwon lafiya na gasar wasannin Olympics ta Beijing.

A gun taron ayyukan shugabannin hukumomin kula da harkokin kiwon lafiya na duk kasar Sin da aka shirya a wannan rana, Chen Zhu ya ce, za'a aiwatar da tsarin sa ido har na tsawon awoyi 24 a sassan kula da harkokin kiwon lafiya. Ya cigaba da cewar, kamata ya yi a tafiyar da ayyukan bada tabbaci ga ingancin abinci da tsabtar ruwan sha yadda ya kamata, da hana shan taba a wuraren taron jama'a, da kara sa ido kan abubuwa masu hadari sosai. Mr. Chen ya kuma kara da cewar, a fannin bada tabbaci ga ingancin magunguna, ba kawai za'a bada tabbaci ga ingancin magungunan da 'yan wasa, da masu horas da su, da alkalan wasa, da jami'ai za su yi amfani da su ba, hatta ma za'a tabbatar da cewar, 'yan wasa ba za su sha wani maganin dake kunshe da abubuwan kara kuzari bisa kuskure ba.(Murtala)