Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-17 16:33:45    
Za a yi binciken ingancin abinci da a samar domin wasannin Olympic a babban filin jirgin sama na Beijing

cri
Tun daga ran 16 ga wata, kamfanin abinci na babban filin hedkwatar kasa ta Beijing zai shafe kwanaki 24 yana aiwatar da ayyukan bincike kan ingancin abincike da za a samar domin wasannin Olympic, bi da bi zai yi bincike kan dukkan wuraren cin abinci da yawansu ya kai 116 a gine-ginen babban filin jirgin saman.

Wani jami'in wannan kamfani ya bayyana cewa, a lokacin binciken, za a yi bincike a kan yadda wuraren cin abincin ke samar da abinci mai inganci a gine-ginen babban filin jirgin saman, don gano abubuwan da ke kawo illa ga ingancin abinci, ta yadda za a ba da tabbaci ga samar da abinci mai inganci a dukan wuraren cin abinci na babban filin jirgin saman.

Bisa shirin da aka tsara, za a kawo karshen dukan ayyukan binciken a ran 10 ga watan gobe. (Halilu)