A wata unguwar da aka fi samun 'yan kabilar Hui a birnin Jinan, babban birnin lardin Shandong da ke gabashin kasar Sin, akwai wani dakin cin abinci irin na kasar Indiya, wanda shi ne dakin cin abinci irin na Indiya daya tak a Jinan. A ko wace rana, mutane da yawa na gida da na waje suna ta cin abinci a nan, kasuwa na ci sosai. Yanzu bari mu shiga wannan dakin cin abinci mai suna furen Jasmine, wato Moli a bakin Sinawa tare, inda za mu kara saninmu kan halayen musamman na kasashen waje da kuma yin hira da masu dakin cin abinci 2, Shadi Abu Zarqa, wani dan Palesdinu, da kuma Naveed Asghar, wani dan kasar Pakistan.
Da zarar shiga dakin cin abinci na Moli, sai a sansani kamshi irin na Indiya da kuma kamshin Curry da aka ajiye a cikin abinci. Sa'an nan kuma, an hada zane-zane da katunan gaisuwa game da ni'imtattun wurare na kasashen Indiya da Pakistan a kan bango. A cikin talibijin kuwa, an nuna shirye-shirye kan raye-rayen da 'yan mata na Indiya suke yi. Sabis din da ke sanye da tufafin irin na Indiya suna yin hidima ga wadanda suke ci abinci a wannan dakin cin abinci. Mutane sun iya kallon tsantsar raye-raye na Indiya, kuma masu amfani da harsuna daban daban sun iya yin hira da juna cikin farin ciki.
A cikin dakin cin abincin, mun ga Shadi, shi ne abokin arzikin mai dakin cin abincin na yanzu, shi ne kuma mai dakin cin abincin na farko. Game da dalilin da ya sa ya bude wannan dakin cin abinci, Shadi ya gaya mana cewa, abokansa da yawa sun zo daga Pakistan da Indiya, ba su saba da abinci na Shandong ba, shi ya sa ya bude wannan dakin cin abinci domin sayar da abinci irin na Indiya. Yanzu ba mutanen Indiya da Pakistan kawai ba, mutane na sauran kasashen duniya su ma su kan ci abinci a nan.
Yanzu Shadi ya yi shekaru 4 ko fiye yana zama a Shandong, sannu a hankali ya fara son cin abinci irin na kasar Sin, haka kuma, al'adun kasar Sin mai dogon tarihi ya jawo hankalinsa sosai. Shadi ya ce, a lokacin da yake yin kasuwanci a kasar Sin, ya sami gatanci da yawa bisa manufofin gwamnatin, shi ya sa kasuwa na kara ci sosai a dakin cin abincinsa. Yanayi ya yi kyau a Shandong, kuma akwai tsabta sosai a birnin, mutane na da kirki sosai, shi ya sa yana son ya ci gaba da zamansa a Shandong.
Shadi yana jin nishadi a Shandong, ya kuma sami sabbin abokai da yawa. Yau da rabin shekara da ya wuce, wani abokinsa wato Naveed ya maye gurbinsa, ya zama mai dakin cin abincin na biyu. Pakistan da Indiya na makwabtaka da juna, suna da al'adar cin abinci iri daya da kuma al'adar zaman rayuwa kusan iri daya. Shi ya sa Naveed ya gwanance wajen tafiyar da dakin cin abinci irin na Indiya. Wannan dan kasar Pakistan ya yi karin bayani da cewa, kayayyakin yaji da kuma wasu danyun abubuwan abinci aka shigo da su daga Indiya da Pakistan kai tsaye, kuma dukkan kuku-kuku sun zo daga Indiya ko kuma Pakistan. Saboda ana dora muhimmanci kan ingancin abinci a wannan dakin cin abinci, shi ya sa karin mutane na gida da na waje sun zo dakin cin abinci na Moli domin dandano abinci iri daban daban na Indiya.
|