Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-16 21:59:12    
An riga an daidaita matsalar ruwan sha daga manyan fannoni dake addabar mutanen da bala'in girgizar kasa ya galabaitar a lardin Sichuan

cri
Wata majiya daga wajen taron manema labaru da gwamnatin lardin Sichuan na kasar Sin ta shirya yau 16 ga wata ta ce, yanzu haka a lardin, an riga an daidaita matsalar ruwan sha daga manyan fannoni wadda ke addabar mutanen da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su, haka kuma, an riga an soma samar da ruwan sha kamar yadda ya kamata ga yankunan dake fama da bala'in girgizar kasa, ban da tsohon garin Beichuan kawai.

A gun taron manema labarun, darektan ofishin watsa labaru na gwamnatin lardin Sichuan Hou Xiongfei ya bayyana cewar, zuwa karfe 7 da daren jiya 15 ga wata, ta hanyar farfado da ayyukan ruwan sha cikin gaggawa a kauyuka, da gina sabbin ayyukan samar da ruwa da injunan tsabtace ruwa a gida, gaba daya dai akwai mutanen da yawansu ya wuce miliyan 5.6 wadanda suka samu ruwan sha ba tare da wata matsala ba.

A gundumomin yankunan dake fama da bala'in girgizar kasa, yawan mutanen da suka samu ruwan sha cikin gaggawa ya zarce kashi 98 daga cikin dari, gaba daya dai akwai mutane dubu 910 wadanda suka samu ruwan sha kamar yadda ya kamata.(Murtala)