Bayan da mummunan bala'in girgizar kasa ya auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin a watan jiya, samari na kasar Sin sun nuna himma wajen shiga aikin yaki da bala'in don ceton jama'a, sun nuna jaruntaka. Haka kuma yayin da wasu kafofin watsa labaru na kasashen yamma suke yada labarain karya a kan gurgunta harkokin yawo da fitilar wasannin Olympic na Beijing a kasashen ketare, samarin kasar Sin sun nuna himma wajen ba da kwarin gwiwa ga kasarsu, kuma sun nuna babban kishin kasa. Yawancin kafofin watsa labaru suna ganin cewa, samarin kasar Sin suna kara kwarewa wajen yaki da kalubale, kuma suna nuna jan hali wajen sauke da nauyin da ke bisa wuyansu.
Malam Dong Chengliu wanda aka haife shi a shekarar 1981 wani manomi ne na garin Yingxiu na gundumar Wenchuan da ke a kudu maso yammacin kasar Sin. Bayan aukuwar mummunar girgizar kasa a garin Yingxiu a watan jiya, Malam Dong ya zama wani mai aikin sa kai bisa burinsa, ya kan yi aiki mai yawa a cikin ofishin shugabanci ta wucin gadi. Ya bayyana cewa, "na kan tashi daga barci da karfe shida na safiyar ko wace rana. Muna shan wahala wajen samun ruwan sha, muna kawo ruwa daga wani wuri mai nisa sosai. Na kan tuka motar tankin ruwa zuwa wurin don kawo wa jama'a ruwa. Na taba tuka manyan motoci masu daukar kaya da fasinja da sauransu don jigilar kayayyaki da masu jin raunuka. Ina zuwa wurare daban daban don yin abubuwan da ake bukata. Na koyi abubuwa da yawa daga wajen yaki da girgizar kasar.
Bayan aukuwar girgizar kasar, hali nagari da samarin kasar Sin suka nuna ya faranta rayukan mutane kwarai. Malam Zhang Tong, wani jami'in lardin Sichuan ya bayyana cewa, daga cikin mutane miliyan daya na kasar Sin wadanda suka yi rajistar neman zama masu aikin sa kai, yawancinsu samari ne. Ya ce, "mun kafa cibiyoyin daukar masu aikin sa kai a ko ina cikin lardin Sichuan, ta yadda samari masu aikin sa kai za su iya shiga aikin yaki da bala'in don ceton jama'a. Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka yi, an ce, daga cikin mutane miliyan 1.1 wadanda suka yi rajistar neman zama masu aikin sa kai, yawancinsu samari ne. Samari sun iya nuna jaruntaka wajen shiga aikin yaki da bala'I a lokaci mai muhimmanci."
Ban da wannan kuma, samari na kasar Sin sun nuna kishin kasa sosai a lokacin da aka gamu da bala'in ruwa da dusar kankara a kudancin kasar Sin a farkon shekarar nan, kuma a cikin tashe-tashen hankulan da masu laifuffuka suka yi a watan Maris a birnin Lhasa, fadar gwamnatin jihar Tibet mai ikon aiwatar da harkokin kanta. Haka kuma yayin da ake yawo da fitilar wasannin Olympic na Beijing a dukan duniya, daliban kasar Sin da ke karatu a birnin London da Paris da San Francisco da sauransu sun shirya taron zaman lafiya, inda suka jinjina tutocin kasar Sin da na wasannin Olympic don taya murnar yawo da fitilar wasannin Olympic.
Malam Wan Chaoqi, ministan Organization na kwamitin tsakiya na kungiyar samari 'yan kwaminis ta Sin yana ganin cewa, daga al'amuran da yawa da suka faru, an gano cewa, samarin kasar Sin a zamanin yau sun sami kwarjini sosai. Ya kara da cewa, "tun farkon shekarar nan, manyan al'amura da abubuwa masu tsanani da yawa sun auku a kasar Sin. Bayan haka hali nagari da samari suka nuna sun mayar da kyakkyawan martani ga shakkar da mutane da yawa ke nuna musu. Samarin sun nuna kyakkyawan burinsu na sauke nauyin da ke bisa wuyansu. Muna alfahari da su. Samari na zamanin yanzu sun sami kwarjiya da amincewa daga wajen jama'a." (Halilu)
|