Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-16 20:42:47    
Ana gudanar da ayyukan tsugunar da mutane, da na sake raya yankuna bayan girgizar kasa kamar yadda ya kamata a lardin Gansu

cri

Bayan da aka samu babbar girgizar kasa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan a ranar 12 ga watan Mayu, lardin Gansu da ke makwabtaka da lardin Sichuan, ya zama yanki mafi girma na biyu da ya yi fama da bala'in. Mataimakin shugaban lardin Feng Jianshen ya bayyana a yau 16 ga wata a nan birnin Beijing cewa, yanzu ana gudanar da ayyukan tsugunar da mutane da sake raya yankin bayan bala'in kamar yadda ya kamata a lardin Gansu.

Mr. Feng Jianshen ya ce, ya zuwa ranar 14 ga wata, gwamnatin kasar Sin ta bayar da kudaden da yawansu ya kai kudin Sin RMB Yuan miliyan 4884, lardin Gansu ya samu taimakon kudi da na kayayyaki da ke da darajar kudin Sin RMB Yuan fiye da biliyan 1.1. Bayan haka kuma, an riga an kawo karshen aikin tsara shirin tsare-tsaren sake raya birane da garuruwa bayan bala'in a lardin Gansu. (Bilkisu)