Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-16 16:40:43    
An kammala aikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a birnin Chongqing nasara

cri

A ran 16 ga wata da safe, an kammala aikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a birnin Chongqing dake kudu maso yammacin kasar Sin cikin nasara.

An fara mika wutar a filin Jinshan na birnin Chongqing, kafin bikin fara mika wutar, dukkan mutane sun nuna ta'aziyya ga mutanen da suka rasa rayukansu a bala'in girgizar kasa na gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan har minti daya.

Zakarar wasan darar chess na kasar Sin ta duniya Gu Li ya zama mai mika wuta na farko, daga nan ne, an fara mika wutar a birnin Chongqing. An je babban titin Jinyu da babbar hanyar Yuanyang da wurin Zonglvquan da sauran wurare. Tsawon hanyar da aka mika wutar a kai ya kai kilomita kimanin 17, masu mika wutar 208 sun shiga cikin wannan aiki.

A karfe 10 da minti 40 da safe, mai mika wutar na karshe kuma zakarar wasan dambe na kasar Sin Li Bing ya cinna kwanon wutar dake babban dakin taro na jama'ar Chongqing, an kammala aikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a birnin Chongqing cikin nasara.

Daga ran 17 zuwa ran 19 ga wata, za a cigaba da mika wutar a jihar Xinjiang dake yammacin kasar Sin.(Lami)