
Yau ran 16 ga wata da karfe misali 8 da safe, an fara mika wutar wasannin Olympic na Beijing a birnin Chongqing.

An fara mika wutar a filin Jinshan na birnin Chongqing, kafin bikin fara mika wutar, dukkan mutane sun nuna ta'aziyya ga mutanen da suka rasa rayukansu a bala'in girgizar kasa na gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan har minti daya.

Tsawon hanyar da aka mika wuta a kai zai kai kilomita kimanin 17, masu mika wutar 208 za su shiga cikin wannan aiki. Shahararren 'dan wasan darar chess na kasar Sin kuma zakarar wannan wasa ta duniya Gu Li ya zama mai mika wuta na farko.(Lami)
|