Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-15 19:52:21    
Kudin taimakon da masana'antun masu jarin waje da na Hong Kong da Macao da Taiwan suka bayar don yaki da bala'in girgizar kasa ya yi yawa

cri
Bisa labarin da wakilin gidan rediyo kasar Sin ya aiko mana, an ce, ya zuwa ran 13 ga wata, gudummowar kudi da ta kayayyakin da masana'antu masu jarin waje da manyan masana'antun kasa da kasa da masana'antun Hong Kong da Macao da Taiwan suka bai wa wuraren kasar Sin da bala'in girgizar kasar ya shafa, ta kai kimanin kudin Sin Yuan biliyan 3 da miliyan 661.

Bisa labarin da aka samu daga hukumomin kula da harkokin kasuwanci na wasu jihohi da manyan birane na kasar Sin da kungiyar masana'antu masu jarin waje ta kasar, an ce, bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka yi, an ce, masana'antu masu jarin waje da manyan masana'antun kasa da kasa da masana'antun Hong Kong da Macao da Taiwan sun riga sun ba da gudummowar kudi da ta kayayyaki da darajarta ta kai kimanin kudin Sin Yuan biliyan 3 da miliyan 661, daga cikinsu, yawan kudin gudummowar da suka bayar ya kai kudin Sin Yuan biliyan 3 da miliyan 39, haka kuma gudummowar abinci da magungunan sha da kayayyakin asibitoci da tantuna da sauransu ta tashi daidai da kudin Sin Yuan miliyan 622. (Halilu)