Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, fitilar wasannin Olympics na Beijing ta sauka a kyakkyawan birnin Buenos Aires, hedkwatar kasar Argentina a ranar 11 ga watan Afrilu na shekarar da muke ciki. Akwai mutane 80 masu dauke da wutar wasannin sun shiga wannan harkar yin yawo da fitilar wasannin. Mr. Manuel Contepomi, shahararren dan wasan kwallon rugby na kasar Argentina yana daya daga cikinsu.
Har sau uku ne Mr. Manuel Contepomi ya shiga gasar cin kofin duniya tawasan kwallon rugby bisa sunan kasar ta Argantine. Da shi da kuma dan uwansa sun zamo shahararrun taurarin wasan kwallon rugby na kasar. Ina ba a manta ba, kungiyar kasar Argentina ta zo ta uku a gun gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon rugby da aka gudanar a kasar Fransa. Wanannan dai maki mafi kyau ne da kasar Argantina ta samu a gun gasar tsakanin kasa da kasa a cikin tarihin wasan kwallon rugby. To, da yake Mr. Contepomi ya nuna gwaninta da kuma bada babban taimako ga sha'anin wasannin motsa jiki na Argentina, shi ya sa aka zabe shi a matsayin mai dauke da tocilan na wasannin Olympics na Beijing.
Lallai karo na farko ne da aka yi yawo da tocilan wasannin Olympics a kasar Argentina, wadda kuma ita ce daya tilo a matsayin wata kasa dake yin amfani da harshen Spain. Don haka ne, Mr. Contepomi ya darajanta wannan kyakkyawar dama da ya samu. Yana mai cewa: ' Na yi alfaharin samun damar daukar nauyin zagayawa da tocilan wasannin Olympics. Gudanar da wasannin Olympics da kuma yin yawo da tocilan wasannin, wani lamari ne dake janyo hankulan jama'ar duk duniya. Akwai 'yan wasa da dama da suka yi alla-allar shiga harkar yawo da tocilan wasannin'.
A yayin da Mr. Contepomi yake tabo magana kan alamar kasar Sin ciikin zuciyarsa, ya yi farin ciki da fadin cewa, tuni yau da shekaru goma da suka gabata, ya taba kawo ziyara nan kasar Sin, inda ya ga kasar na kasancewa tamkar wata kasa ce ta zamani. Yana mai cewa: ' Kasar Sin ta samu ci gaba da saurin gaske a fannin wasannin motsa jiki duk da cewa tana baya-baya a fannin wasasannin kwallon rugby.Amma na yi imanin cewa, irin wannan wasa zai samu karbuwa sannu a hankali a kasar Sin, kuma ina fatan za a shigar da shi cikin ajandar wasannin Olympics'.
A matsayin wani dan wasa, shi Mr. Contepomi ya dauka cewa, kasar Sin na da kyakkyawar makoma a fannin bunkasuwar wassu ayyukan wasa. Ya ce, daga T.V. ne nakan sami labarin cewa kasar Sin ta taba samun lambobin yabo da yawa a fannin wasan lankwashe jiki wato gymnestics a Turance, da wasan guje-guje da tsalle-tsalle da kuma wasan ninkaya da dai sauransu. Ko da yake a da kasar Sin ba ta yi fice a duniya wajen samun kyakkyawan sakamako a fannin wasannin motsa jiki ba, amma a yanzu haka dai ta riga ta kama gaba a duniya a fannin samun lambobin yabo.
Tare da yin la'akari da karatowar wasannin Olympics na Beijing, Mr. Contepomi ya kuma nuna fatan alheri ga wannan gagarumar gasa. Yana mai cewa: ' Gasar wasannin Olympics, wata gagarumar gasa ce ta wasannin motsa jiki dake bisa matsayi na farko a duniya. Da zuciya daya ne nake fatan za a gudanar da wasannin Olympics na Beijing da kyau kamar yadda aka gudanar da ita a da. Kuma ina begen bikin bude wannan gagarumar gasa. Na hakkake cewa, jama'ar kasar Sin na da karfin da take da shi na gudunar da wata gasar wasannin Olympics da za ta burga jama'ar duk duniya'. (Sani Wang)
|