Lubabatu: A nan sashen Hausa, ban da ma'aikata Sinawa, akwai kuma wasu ma'aikata Hausawa da suka kware a kan harshen Hausa wadanda muka gayyace su daga kasashen Nijeriya ko Nijer. To, idan ba ku manta ba, a shirinmu na baya, mun yi hira da Balarabe Shehu Ilelah da Lawal Mamuda, wato ma'aikatanmu biyu da suka zo daga Nijeriya, inda suka bayyana mana yadda suke gudanar da aiki a nan sashen Hausa da kuma yadda suke zaman rayuwa a nan kasar Sin. To, idan mun ambaci sunan Baba Dan Lawal Hamza Darazo, watakila masu sauraronmu kuna iya tunawa da shi, sabo da shi ya kasance tsohon ma'aikacin sashen Hausa, kuma ya shafe tsawon shekaru biyu yana aiki a nan sashen Hausa. To, ga shi kwanan baya, wakilinmu a birnin Ikko, wato Bello, ya sami damar yin hira da shi ta wayar tarho.
Baba:Hello.
Bello:Hello, malam Hamza, sannu.
Baba:Madallah, sannunka malam Bello.
Bello:Ko za ka iya gabatar da kanka zuwa ga masu sauraronmu?
Baba:Sunana Baba Dan Lawal Darazo, wanda na yi aiki a sashen Hausa daga shekarar 1998 zuwa ta 2000. An haife ni a garin Darazo da ke jihar Bauchi, a kasar Nijeriya. A yanzu haka ina aiki a sashen yada labaru ne na gwamnatin jihar Bauchi.
Bello:Wasu tsoffin masu sauraronmu har zuwa yanzu ba su manta da muryarka ba, sabo da ka taba aiki a sashen Hausa na cikin tsawon shekaru biyu. Masu sauraronmu za su so su san dalilin da ya sa ka je birnin Beijing aiki.
Baba:To, a gaskiya, dalilin da ya sa na je Beijing, sashen Hausa, (shi ne), tun ina yaro, tun ina dan karami, akwai mujallu da kasidu da hotuna da rediyon kasar Sin yake aikowa ga masu sauraro, za ka ga hotunan shugaba Mao a wancan lokaci, To, ire-iren wadannan su ne suka ba ni sha'awa a kan yadda nake ganin kasar Sin a hotuna. To, ana nan ana nan kullum burina da tunanina da mafarkina shi ne Allah ubangiji ya kai ni kasar Sin. Sannu a hankali sai Allah ya sa na samu aiki a sashen Hausa na rediyon kasar Sin, yadda na zamanto kwararre a kan harshen Hausa, kuma na yi musu aiki na kusan shekaru biyu ke nan da na zauna a birnin Beijing.
Bello: To, a wadannan shekaru biyu da kake can Beijing, yaya mutanen Sin da abokan aikinka Sinawa suka karbe ka, ko akwai abin da ya burge ka?
Baba: E, abubuwan da suka burge ni a kan kasar Sin suna da yawan gaske, idan na ce zan bayyana muku su lokaci ma ba zai isa ba, sai dai abu guda bari in shaida muku cewa, farkon tunanina, na dauka mutanen kasar Sin suna kyamar jama'a kamar yadda ake samu a Amurka da Jamus da wasu kasashen Turawa. To, da na je sai na ga in kai baki ne kuma sha'awarka ake yi, kuma yarensu da al'adunsu da yanayin zaman takewarsu ya ba ni sha'awa sosai, abin farin ciki shi ne yadda suke daukan aiki da yadda suke daukan jama'a da abubuwan da aka samu don cigaba a kasa, wato kowa ka same shi a kasar Sin, shi hidimar gabansa yake yi, dan kasuwa ne yana aikin kasuwancinsa, ma'aikacin gwamnati yana aikin gwamnatinsa, in direban taxi ne yana tukin mota ka'in da na'in tsakar dare, idan manoma ne, su ma noma suke yi na ban sha'awa to, ka ga abubuwan da na ga a kasar Sin, shi ya sa na ce maka, suna da yawan gaske wadanda suka ba ni sha'awa. Gaskiya suna da yawan gaske.
Bello:Masu sauraronmu za su so su san lokacin da kake can birnin Beijing, ko ka saba da yanayi da abinci da dai sauransu a wurin?
Baba:To, ka san, da farko, dole a sami matsala. Farko babban abin da ya same ni a kasar Sin, (shi ne) farkon isana na isa a lokacin sanyi ne, sabo da a nan Nijeriya, kuma a jihar Bauchi, temprature, wato yanayin zafi din, haskensa ba ya haskawa , bai wuci a kan ma'auni da maki 35,38, tun lokacin sanyi ne, za ka samu tsananinsa ya zo 17 ne. To, ranar na sauka a birnin Beijing a lokacin sanyi din, yana kan maki na kasa, har da maki 5, to, ka gani sanyi ne wanda ban taba jinsa ba har a rayuwata. Kuma wannan abu ya dame ni daga farko,amma sannu a hankali tun da zama ne ba na kwana daya ko kwana biyu ba, sabo da haka, na hadiye shi na shanye na ci gaba. Abincinsu ba shakka, daga farko na ziyarci na je na samu shinkafa da miya kamar yadda aka sani a kasar Hausa, kuma abincinsu za ka samu taliya, za ka samu na dankali da gwaza, za ka samu abubuwa da yawa, ka ga abubuwa da farko na dan shan wahala, amma sannu a hankali, har yau nan da nake Nijeriya, ina burin cin abubuwa da yawa na kasar Sin. Abincinsu da yawa suna ba ni sha'awa, kamar wani abin da ake kira "mantou", da abubuwa da yawa suna ba ni sha'awa sosai.
Bello: Ko ya kasance da wasu wurare a kasar Sin da ka taba yin ziyara, kuma har zuwa yanzu ba ka iya manta da su?
Baba:E, gaskiya na je wurare a kasar Sin, na farko, rediyon kasar Sin da nake kasar Sin ya tura ni na dauko masa labaru a wani biki na shida na duniya na wasan Shaolin Wushu, da aka yi a sashen tsakiyar kasar Sin, wato lardin Henan, birnin Zhengzhou ke nan, a nan muka je muka dauko labaru na wajen kwana 9. Bayan nan ma kuma, da 'yan wata 7, a nan birnin Zhengzhou, an sake yin biki na furanni, na sake zuwa na dauko labarai. Bayan haka, akwai wasu wurare da na ziyarta, kamar su Wuhan da Shanghai da dai makamantansa, na je ne domin ziyara, domin gani da ido.
Bello:Gaba daya me za ka ce game da zamanka a kasar Sin?
Baba: Gaskiya, zaman da na yi a kasar Sin ya shiga jikina sosai, sabo da ba zan manta da kasar Sin a rayuwata ba, sabo da cudanya da na yi da mutanen can. Na yi yawo cikin birnin Beijing, kuma na ga zan yi yawo a tsakar dare ba ka tunanin kome ba, ba ka tunanin ko wani barawo, ko wasu za su tare ka a tsakar dare, za ka tashi karfe daya karfe biyu karfe uku, ka yi yawo cikin birnin Beijing, ba ka tunanin kome, ka ga wannan abu ne da ban iya mantawa da shi ba. Sa'an nan, ma'aikatan sashen Hausa da na yi aiki da su, sun ba ni sha'awa sosai, akwai Sanusi, akwai Umaru, akwai Ali, akwai Dogonyaro, akwai kuma Halilu, wanda lokacin da na je shi ne shugaban sashen hausa, akwai Usman, akwai Halima da Asabe da Hadizah da Jamila, dukansu na ji dadin aiki da su sosai, kuma na samu karuwa, sun samu karuwa a gare ni. Har zuwa yanzu ina tunanin kasar Sin, har ma a nan karkararmu, ana kira mana Basine.
Lubabatu:To, masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau, amma kada ku manta, a makon gobe war haka, za mu ci gaba da kawo muku shirye-shiryenmu na "waiwaye adon tafiya", da haka ni Lubabatu daga nan Beijing ke cewa, "sai Allah ya kai mu ranar Jumma'a mai zuwa. (Lubabatu)
|