Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-13 16:33:49    
Hukumar nazari ta kasar Amurka ta gabatar da wani rahoto domin yin tunani sosai kan siffar kasar Amurka a idon kasashen duniya

cri

A ran 12 ga wata, shahararriyar hukumar bincike da nazari wato PEW ta gabatar da wani rahoto kan siffar kasar Amurka a idon kasashen duniya. Rahoton ya ce, siffar kasar Amurka ta kara lalacewa tun bayan yakin Iraki, amma sabo da babban zaben shugaban kasar da aka fara gudanarwa daga shekarar bara shi ya sa an kyautata wannan mummunar siffa kadan.

Babban edita mai kula da harkokin nazarin manufofin diplomasiyya na hukumar PEW Mr. Moises Naim yana ganin cewa, ma'aunoni iri biyu da kasar Amurka take daukawa a manufofin diplomasiyya ya zama wani babban dalilin da ya sa duk duniya yake adawa da ita, ya ce,

'Kasar Amurka tana daukar ma'aunoni biyu kan manufofin diplomasiyya, ga wani misali, kasar Amurka ta yi amfani da batun hakkin 'dan Adam domin yada ra'ayoyinta a sauran kasashe. Wannan ya gamu da adawa daga duk duniya. Wadannan kasashe su kan yi tambaya cewa, me ya sa kasar Amurka ta tilasta wa sauran kasashen da su gudanar da ka'idojin cinikayya daban daban, amma ita kadai ba ta gudanar da su ba ?'

Mr. Richard Wike shi ne shugaban shirin bincike kan siffar kasar Amurka a idon kasashen duniya daga hukumar PEW. Ya ce, ko shakka babu, yakin da kasar Amurka ta tayar kan kasar Iraki a shekarar 2003 ya lalata siffar Amurka, amma wannan ya zama dalili daya kawai na lalacewar siffar kasar Amurka. Ya ce,

'Lalacewar siffar kasar Amurka ya zo ne daga manufofin diplomasiyya da take gudanarwa, wadanda sauran kasashen duniya suke adawa da su, da kuma yakin Iraki, da kuma ra'ayin daukar matakai na gefe daya kan harkokin duniya.'

Ban da wannan kuma, tabarbarewar tattalin arziki na kasar Amurka ta kara lalata siffarta a duk duniya. Game da haka, Mr. Moises Naim ya ce,

'Tattalin arziki da kuma manufofin da kasar Amurka take gudanarwa za su kawo tasiri ga duk duniya. Kasashen duniya suna ganin cewa, kasar Amurka ta zama uwar laifi da ke haddasa tabarbarewar tattalin arzikin duniya, wannan ba shakka ko kadan. Mutanen duniya ba su sani ba, ya kasance da dalilai da yawa da ke haddasa lalacewar tattalin arzikin duniya.'(Danladi)