
Ran 13 ga wata, an sami nasarar mika wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Kaili na lardin Guizhou a kudu maso yammacin kasar Sin.

Birnin Kaili, babban birnin yankin Qiandongnan na kabilun Miao da Dong na lardin Guizhou. Tsawon hanyar mika wutar a Kaili ya kai misalin kilomita 28.9, an kuma raba hanyar zuwa kashi 3. Wuraren da ke gefunan hanyar mika wutar sun nuna al'adun kananan kabilu a yankin Qiandongnan, sun kuna nuna halin musamman na Kaili, wato kabilu da yawa suna zaman cude-ni-in-cude-ka cikin jituwa.
Masu rike da wutar 208 sun shiga aikin mika wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a Kaili.
A gun bikin kaddamar da aikin, dukkan wadanda suka shiga aikin sun yi tsit har minti daya domin nuna alhini ga wadanda suka rasa rayukansu a cikin mummunar girgizar kasa ta Wenchuan a Sichuan. Masu rike da wutar da kuma rukunoni daban daban na Kaili sun ba da kudaden taimako ga wuraren da ke fama da bala'in.
Ran 14 ga wata, za a mika wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Zunyi na lardin Guizhou.(Tasallah)
|