Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-12 18:29:55    
Baki samari uku suna zaman jin dadi a kasar Sin

cri

An sami baki samari uku a wani kamfanin tattare da nazarin da bunkasa da kuma kera injuna masu samar da wutar lantarki da karfin iska a birnin Wurumq,babban birnin jihar kabilar Ughur mai ikon tafiyar da harkokin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin.

Ungaro Florence, 'yar Faransa ce. Bayan da ta kammala karatunta na jam'ia a fannin nazarin ilimin samar da wutar lantarki ta zo na birnin Beijing,babban birni na kasar Sin domin aikatarwa, ta niyyata ta yi aikatarwa a nan birnin Beijing ne duk domin babbar sha'awar al'adun kasar Sin da take da shi tun tana karama.

Ta ce"Ina sha'awar kasar Sin tun ina karama, a ganina kasar Sinta sha banban da sauran kasashen duniya,al'adunta ya fi dadewa a duniya, haka kuma tarihinta kuma sun fi arzuta. A ganina kalmar sinanci ta sha banban da na sauran harsuna, kuma tana da kyaun gani. Bayan na kammala karatuna a jami'a ina so in zo kasar Sin domin aiki, ina so in yi zama a kasar Sin. A shekara ta 2003 na karo ilimi na rabin shekara a birnin Beijing. Bayan hakan ina so in yi aiki a kasar Sin, duk da haka ban sami damar aiki a kasar Sin ba,sai na koma gida Faransa na yi aiki."

Miss Ungaro Florence ba ta cika burinta na yin aiki a kasar Sin ba bayan da ta kammala karatunta a jami'a. duk da haka tana ci gaba da fatan samun damar aiki a kasar Sin, ta kan mayar da hankalinta kan bayanan da aka bayar na daukar ma'aikata a kasar Sin cikin shekaru biyu da take aiki a kasar Faransa. Daga baya ta samu dama, bisa gabatarwar da wani amininta ya yi, Miss Florence ta zo birnin Urumqi na jihar kabilar Ughur mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta yi aiki a kamfanin Jinfeng na kimiyya da fasaha.

Ta ce"na yi shekaru biyu ina aiki a Faransa, duk da haka ina so in zo kasar Sin cikin shekarun biyu.na samu dama na yi sallama. Na zo nan kasar Sin in shiga jarrabawan da aka yi mini, aminina ya gaya mini cewa wannan kamfanin da na ke so in shiga kamfani ne dake aiki na fitar da injunan samar da wutar lantarki, ina sha'awarsa, da na ci jarrabawan na zo nan birnin Urumqi in yi aiki a wannan kafani na kimiyya da fasaha ."

Bayan da burinta na aiki a kasar Sin ya tabbatu, Miss Florence ta kamu da sabuwar matsala a zamanta. Masoyinta bai zo nan kasar Sin ba sabod yana tsoron rashin iyawa da magana cikin sinanci. Ta ce"Masoyinta ya yi nazarin harshen Sinanci na tsawon shekaru biyu,yana tsoron yin magana da zuwan kasar Sin. Da ya zo nan birnin Beijing, ya ga amincin da mutanen kasar Sin suka yi mini. Ya fargaba."

Da hakan Miss Florence ita kadai take aiki a kasar Sin domin tabbatar da makasudinta, ta yi rabuwa da masoyinta. A ganinta, ta dauki wannan mataki ne duk domin tana kaunar kasar Sin da sha'anin kiyaye muhalli.

Ta ce" kasar Sin ta bunkasa da saurin gaske, tana bukatar karin makamashi, ina tsammani ba za a iya ci gaba da amfani da kwal da man fetur da kuma gas ba, ina so a samar da wutar lantarki da karfin iska, domin kuwa wannan hanyar da ake bi ba ta gurbata muhalli ba."

A cikin farkon watanni biyu na saukarta a birnin Urumq na jihar kabilar Ughur, birnin Urumq ya dauke hankalinta sabo da akwai harsuna da al'adu na kanana kabilu a cikinsa, ta yi fatan nazarin harsunan kanana kabilu da kara fahimtar al'adunsu.

Ta ce " A cikin jihar Xinjiang da akwai kanana kabilu da dama,ciki har da kabilar Ughur da ta Kazak. Ina sha'awar harshen Ughur, mutanen Ughur sun fi sauran kabilu koyon harshensu, idan zan dade a nan, harshen nan yana da amfani gare ni."

A birnin Urumqi Florence tana da aminai masu fara'a da dama a wurin, ta kan taru da su, da yin raye raye da wasanni tare da kuma rera wakoki.

Mr Feng Yun tana daya daga cikin aminan Florence na kasar Sin. Ita jami'in kula da ma'aikata baki na kamfanin Jinfeng na kimiyya da fasaha. Ta kan shirya ayyuka daban daban duk domin kara zumuncin dake tsakanin ma'aikata na kasar Sin da na ketare.

Ta ce" a lokacin hutu bayan aiki, baki ma'aikata za su iya yin aikace aikace tare da takwarorinsu na sinawa, in yanayi ya yi, sun iya tuka motoci zuwa wurare masu nesa ko su yi hawan duwatsu ko su yi wasan tafiya a kan kankara. Ma'aikatanmu su kan kula da su da yin hira da su. Bisa martanin da suka mayar, an ce suna zaman jin dadi a wannan wurin, sun saba da abincin wuri. Da akwai abinci iri iri da yawa na kanana kabilu da kuma abinci na kasashen yamma, baki ma'aikatan sun dandana dukkan abincin dake akwai a wurin. Kusan a ce ba su da matsala wajen samun abinci da kayan saka da kuma gidajen zama da ababen hawa."

Miss Florence tana sha'awar yawon shakatawa. A duk lokacin da take aiki a birnin Urumqi, ta kan yi yawon bude ido tare da aminanta a lokacin hutu.

Ta ce"Na taba tafi duwatsun Tianshan da Nanshan da kuma kwarin Turfan, ina so in yi yawon bude ido a wurare da dama na jihar Xinjiang, da akwai wurare masu kyaun gani a jihar Xinjiang ina so in je birnin Kash da hamadar Taklamagan da kuma wurin Kanas,wuri ne mai ni'ima da kyaun gani a kudancin birnin Urumqi."

Wasun shekaru sun kure, Florence ta gaya wa wakilinmu cewa 'yan iyalinta da kuma masoyinta za su zo nan kasar Sin a watan Mayu na wannan shekara domin haduwa da ita. Ta tsara wani shirin yawon shakatawa a jihar Xinjiang domin shere su.Ta ce" na yi shirin zagaya da su a kwarin Turfan da birnin Kash da babban tafkin Tianchi da cibiyar birnin Urumqi da kuma garin Daban da kuma masana'antarmu ta samar da wutar lantarki da karfin iska ta yadda su ga abubuwan ke gudanarwa a wannan jihar."

Daga cikin ma'aikatan da suke aiki tare da Florence da akwai wani mutumin da ya zo daga kasar Netherland da ake kiransa Harmen Krediet, shi dalibi ne da ke cikin jami'a ya zo nan jihar Xinjiang domin aikata abin da ya koya, kamar yadda Florence take, Harmen Krediet shi kansa ya zo nan kasar Sin domin aiki.Ya ce"An samar da damar aikatawa da dama cikin shafunan yanar gizo ta internet a jami'ar da nake karatu a ciki, a kan sabunta labarai kowane mako, daga baya na sami labarai dangane da kamfanin Jinfeng."

A halin yanzu Mr Harmen Krediet ya shafe watanni uku da 'yan kai yana aiki da zama a kamfanin Jinfeng na kimiyya da fasaha dake jihar Xinjiang, wa'adinsa na aikatarwa zai kusan cikawa. Da wakilin gidan rediyonmu ya tambaye shi me ya burge shi a jihar Xinjiang, Harmen ya ce abin da ya fi burge shi a jihar shi ne abinci mai dadin ci a wannan jiha.  Ya ce"ina kaunar abincin kasar Sin sosai, abincin jihar Xinjiang ya sha banban da na sauran jihohi na kasar Sin domin a wannan wurin ba ma kawai da akwai tasiri na sauran wuraren kasar Sin har ma da akwai tasirin kasar Kazakstan."

Tare da buri daya, Mr Erik de Vrij da ya zo daga kasar Netherland ya yi aiki a kamfanin Jinfeng na kimiyya da fasaha dake a birnin Urumqi. Kafin ya zo nan kasar Sin ya yi aiki a kamfanin sufuri ta jiragen ruwa a tekuna na kasar Netherland, daga baya ya yi aiki a wani kamfanin ba da hidima kan samar da wutar lantarki da karfin iska.Wata rana da ya yi balaguron kasuwanci zuwa birnin Urumqi, ya gamu da kamfanin Jinfeng na kimiyya da fasaha, makomar ayyukan kamfanin Jinfeng ta dauke hankalinsa. Da ya koma gida ya yi murabus daga aikinsa ya zo nan kasar Sin domin aiki a kamfanin Jinfeng har ya zama manaja na sashen kula da harkokin ketare na kamfanin.

Ya ce" Dalilin da ya sa na zo nan kasar Sin shi ne kasar Sin ta kasance wata babbar kasuwar duniya dake bunkasawa da saurin gaske. Na taba aiki a matsayin mai binciken kasuwanni a wani kamfanin Turai, na ji al'amura da dama da suka wakana a kasar Sin, alali misali, ci gaban tattalin arziki,a wani bangare ina sha'awar kasar Sin sosai, a wani bangaren daya fannin da nake kwarewa yana biyan bukatun kamfanin Jinfeng.Ina so in zama wani mamba na kamfanin Jinfeng.in yi kokari da ma'aikatan kasar Sin wajen kera injuna masu inganci na samar da wutar lantarki cikin amfani da karfin iska. Na sane da cewa a ganin wasu kasashen Turai da na yamma, kayayyakin da kasar Sin ta fitar ba su da inganci,wannan shi ne dalilin da ya sa na zo kamfanin Jinfeng in yi aiki a ciki domin in shaida musu ainihin halin da kasar Sin ke ciki wajen fitar da injuna masu inganci."

Hanyar da Erike ke bi cikin nutsuwa wajen aiki ta samu karbuwa daga ma'aikatan kamfanin. Haka kuma suna cikin zaman jin dadi sabo da tsarin kula da ma'aikatan da wannan kamfanin ke aiwaitar da shi. Bisa bayanin da Mr Erik ya yi, an ce kowace shekara kamfanin na samar da lokacin hutu ga kowane ma'aikacinsa da su koma gida domin haduwa da iyalinsa, a cikin wannan lokaci an ba su albashi da kudin alawas da sauran abubuwan more zaman rayuwa, lalle suna zama kamar a gidajensu.