Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-12 18:26:38    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri

Dan caca yana buya domin gudun biyan bashi.Wani dan babbar makarantar sakandare mai suna Xiao Hua wanda ya ke da shekaru 17 da haihuwa ya yi bakin ciki sosai sabo da yawan bashi da ya ci a sanadin cacar da ya shiga kan wasan kwallon kafa,yawan bashin da ya ciwo ya kai kudin Sin RMB yuan sama da dubu takwas.Wannan al'amari ya faru ne a gundumar Wenchang na lardin Hainan. Yaron Xiao yana tsoron tafi makaranta domin gudun ganawa da masu bin bashi. Domin masu bin bashi sun ce idan ba ya biya bashi za su buge shi.Iyayen Xiao ba su da aikin yi cikin shekaru da dama,har yanzu dai ba su san me ya same dansa ba.lauyoyi na wuri sun kawo wa yaron da ubansa shawara cewa su gabatar da batu ga 'yan sanda.

Wani mutum ya bugu da giya. An sami wani dalibi mai suna Chen a birnin Harbin,babban birnin lardin Heilongjiang dake arewa maso gabacin kasar Sin wanda ya ke da nufin shere 'yan ajinsa wajen iyawa sha giya,daga baya ya sha giya mai yawa har ya bugu aka kai shi asibiti. A ranar talata da dare, tare da 'yan ajinsa guda biyar ya je dakin cin abinci sun sha giya tare har sun sha giya mai karfi wato Liquor kwalbani biyu da giyar beer kwalbani goma. Daga baya Chen ya bugu da giya. Wani likita na makarantar ya ce "wannan batu ba daya kawai da ya faru a makaranta ba tun lokacin da aka fara karatun a farkon shekara.ya kuma kawo shawara ga 'yan makaranta da su kaurace giya domin ta bata lafiyar jiki.

Ana cigiyar wani mutum da ya yi yunkurin yin bashi a banki. "yan sanada na birnin Jilin,babban birnin lardin Jilin na arewa maso gabacin kasar Sin suna nan suna farautar wani mutum da ya yi yunkurin yin fashi a banki tare da wani bom na bogi. Wata rana da safe wani mutum ya zo bankin dake cikin birnin,da ya shiga bankin ya jawo wani abin da yake kiran abin fashewa ne daga jakarsa,ya bukaci ma'aikatan bankin da su ba shi kudin Sin RMB Yuan dubu talatin,ya yi barazanar cewa idan ba su ba shi kudin da yake bukata ba zai rushe banki da kashe dukkan ma'aikatan dake ciki.Duk da haka wani ma'aikaci a cikin banki ya buga kararawa,kuma ya sa loudspeakers na bankin sun yi kara.da jin hakan mai fashi ya gudu.Da isowar 'yan sanda sun gano cewa bom da dan fashi ya yi amfani da shi na bogi ne.

Motoci sun yi cunkuso sabo da hayaki ya turnuke a kan hanyar mota. A kalla dai direbobi guda uku sun ji rauni,daya daga cikinsu mata ce mai juna biyu a cikin wani cunkuson motoci sama da ashirin da aka samu a kan hanyar mota na gundumar Liaozhong dake cikin lardin Liaoning.Matar mai ciki ta yi sa'a da aka kai ta asibitin an yi mata bincike cewa ba kome ya same ta watakila domin babu ci karo mai tsanani yayin da motocin sun yi cunkuso. Wani direba ya ce hayaki ya turnuke a kan hanyar mota ba mu iya gane abin dake kan hanya sosai ba,shi ya sa motocinmu sun yi cunkuso a kan hanya.

Jama'a masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau na labaru masu ban sha'awa. Muna fatan za mu sake saduwa da ku a wannan lokaci na mako mai zuwa.(Ali)