Yau ran 12 ga watan Yuni na shekara ta 2008. Kafin wata daya da ya gabata, an samu bala'in girgizar kasa mai karfin digiri 8.0 na ma'aunin Richter a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan da ya kawo babbar hasara ga rayukan jama'a da dukiyoyinsu. Ya zuwa karfe 12 na ran 12 ga watan Yuni da tsakiyar rana, yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon wannan bala'in ya riga ya kai dubu 69 da 159 tare da mutane fiye da dubu 370 da suka jikkata da mutane fiye da dubu 17 da suka bace.
Bayan aukuwar bala'in girgizar kasa a gundumar Wenchuan, a cikin wani bayani mai suna "kasar Sin, sa kaimi" da kamfanin dillancin labaru na Rasha ya bayar, an ce, yawan bala'un da kasar Sin ta sha ya yi yawa sosai, amma ba ta taba ba da kanta ba. Yau, wato bayan aka samu bala'in girgizar kasa a wata daya da ya gabata, za mu iya jin alfahari da cewa, kasar Sin ta riga ta samu kwarya-kwaryar nasara wajen fama da bala'in girgizar kasa. Yanzu, yankuna masu fama da bala'in suna cikin kwanciyar hankali, an riga an tsugunar da dukkan mutane masu fama da bala'in kamar yadda ya kamata. Hakikanan abubuwa sun shaida cewa, a wannan karo, kasar Sin ba ta fadi ba. Za a tuna da dukkan al'amuran da suka auku a kasar Sin a nan gaba.
"Ina cike da imani cewa, kowace irin matsala ba za ta iya tsorata jama'ar kasar Sin wadanda suke da jarumtaka ba."
Jama'a masu karatu, maganar da kuka ji ita ce maganar da Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya yi lokacin da yake nuna jejeto ga fararren hula da sa kaimi ga sojoji da mutane wadanda suke fama da bala'in girgizar kasa a birnin Shifang na lardin Sichuan. Bayan aukuwar bala'in girgizar kasa a lardin Sichuan, ba tare da bata kowane lokaci ba gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan fama da shi. Ko shugabannin kasar Sin ko kananan jami'an da ke aiki a yankuna masu fama da bala'in, dukkansu sun shiga aikin fama da bala'in da ceto mutane. A waje daya kuma, dukkan sojoji da hukumomin gwamnatin kasar Sin sun hada kansu sosai sun taka muhimmiyar rawa wajen fama da bala'in domin kokarin raguwar hasarar da bala'in girgizar kasa ya kawo mana. Sabo da haka, tabbas ne za a tuna da kokarin da gwamnatin kasar Sin ta yi ba tare da kasala ba a nan gaba.
Bugu da kari kuma, bayan aukuwar bala'in girgizar kasa a Wenchuan, yawan sojoji da 'yan sanda masu dauke da makamai da sojoji farar hula da kasar Sin ta aika da su zuwa yankuna masu fama da bala'in ya kai fiye da dubu dari 1. A dukkan wuraren da ake fama da bala'in, ka iya ganin jikokinsu. Dukkan abubuwan da suka yi sun burge kowane mutum. Tabbas ne za a tuna da muhimmiyar rawar da sojojin kasar Sin suka taka a wannan karo a nan gaba.
"Lokacin da nake rundunar soja, na taba yin aikin ceto. Ina tsammani suna da na'urorin sana'a. Za mu iya tsara shiri mafi kyau wajen ceto mutane."
Jama'a masu karatu, maganar da kuka ji ita ce maganar da wani mutum mai aikin sa kai kuma mai suna Chen Yan ya yi. Lokacin da muke fama da bala'in girgizar kasa, yawan mutane masu aikin sa kai da suka zo daga sana'o'i iri daban daban na dukkan kasar Sin, har kuma daga wasu kasashen duniya ya yi yawa, har yanzu ba a san hakikanin adadinsu ba. Tabbas ne za a tuna da gudummawar da suka bayar a nan gaba.
Bugu da kari kuma, loacin da mu Sinawa muke fama da wannan bala'in, abokai daga kasashen waje, kamar su Rasha da Japan da kasar Koriya ta kudu da Singapore da Jamus da Faransa da Italiya da Cuba sun aiko da kungiyoyinsu na jin kai da na jiyya domin taimakawa kasar Sin. Tabbas ne za a tuna da taimakon da sauran kasashen duniya suka ba mu ba tare da son kai ba a nan gaba.
Muna da imani cewa, a karkashin kokarin gwamnati da jama'a na kasar Sin tare da taimakawar sauran kasashen duniya, tabbas ne kasar Sin za ta samu nasarar karshe a fannin fama da wannan bala'in girgizar kasa.
|