Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-11 20:33:11    
An yi kusan kawo karshen aikin ba da agaji bisa babban mataki wajen likitanci ga wurare masu fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan

cri

A ranar 10 ga wannan wata a birnin Beijing, wani jami'in ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ya bayyana cewa, yanzu, an yi kusan kawo karshen aikin ba da agaji bisa babban mataki wajen aikin likitanci ga wurare masu fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan na kasar Sin, yawancin mutanen da suka ji raunuka ana warkar da su yadda ya kamata. A nan gaba, sassan kiwon lafiya da abin ya shafa za su dauki mtakai daban daban don ba da tabbaci ga rashin yaduwar annoba a yayin da ake gamuwa da babban bala'in.

A gun taron ganawa da manema labaru da aka shirya a wannan rana, kakakin ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin Mr Mao Qun'an ya bayyana cewa, bayan aukuwar lamarin girgizar kasa a ranar 12 ga watan Mayu a lardin Sichuan na lasar Sin, sassan da abin ya shafa na kasar Sin sun riga sun aika mutanen da suka yi aikin likitanci da yin rigakafin yaduwar annoba da masu sa ido wadanda yawansu ya kai dubu 10 ko fiye zuwa wurare masu fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan, sa'anan kuma yawan motocin ambulance da sauran motocin da ake yin amfani da su domin yin rigakafin yaduwar ciwace-ciwace da sa ido ga aikin kiwon lafiya kuma aka tattara su daga wurare daban daban na duk kasar Sin ya kai dubu 2, a sa'I daya kuma an tsara shirin aikin yin rigakafin yaduwar annoba wajen fama da bala'in girgizar kasa da sauran shirye-shirye a jere, ta hakan, ana aiwatar da ayyukan kiwon lafiya yadda ya kamata bayan girgizar kasa. Mr Mao Qun'an ya bayyana cewa, yanzu, an yi kusan kawo karshen aikin ba da agaji wajen likitanci cikin gaggawa kuma bisa babban mataki, yawancin wadanda suka ji raunuka ana warkar da su yadda ya kamata. Sa'anan kuma an kaurar da wadanda suka ji raunuka kuma yawansu ya kai dubu 10 ko fiye na lardin Sichuan zuwa larduna fiye da 20 na duk kasar Sin don warkar da su, sauran wadanda suka ji raunuka sosai ana warkar da su wajen shahararrun likitocin da aka tattara su daga duk kasar Sin a wuri gu daya.

Mr Mao Qun'an ya ci gaba da bayyana cewa, a nan gaba, sassan kiwon lafiya za su kara karfinsu na ba da agajin , za su yi iyakacin kokarinsu don ceton rayukkan wadanda suka ji raunuka, sa'anan kuma za su shirya kungiyoyin likitanci na wurare daban daban da su yi aikin tiyata kan ciwon hakiya da ciwace-ciwacen  mata da sauransu, sa'anan kuma za a kara karfi wajen daidaita cikas da jama'ar da ke zama a wurare masu fama da bala'in girgizar kasa suka samu wajen zuciya.

1 2