Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-11 20:10:03    
Mutanen da suka kamu da cutar shanyewar jiki sun fi saurin mutuwa in ba su samu kulawa daga 'yan iyali da abokai ba

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili na "ilmin zaman rayuwa". Ni ce Kande ke gabatar muku da wannan shiri. A cikin shirinmu na yau, za mu yi muku wani bayani kan cewa, mutanen da suka kamu da cutar shanyewar jiki sun fi saurin mutuwa in ba su samu goyon baya daga 'yan iyali ba.

Bisa wani babban binciken da ma'aikatar kula da kiwon lafiya da 'yan kwadago ta kasar Japan ta gudanar, an ce, game da mutanen da ba su iya samun goyon baya daga 'yan iyali da abokai ba, muddin sun kamu da cutar shanyewar jiki, to yiyuwar mutuwarsu za ta ninka sau 1.5 in an kwatanta da wadanda suke iya samun kulawa daga iyali da abokai.

Bisa bayanin da kafofin watsa labari na kasar Japan suka bayar, an ce, a shekara ta 1993, kungiyar nazari ta ma'aikatar kula da kiwon lafiya da 'yan kwadago ta kasar ta fara gudanar da wani bincike ga mutane masu aikin sa kai kimanin dubu 44 da shekarunsu ya kai 40 zuwa 69 da haihuwa, wanda ya dade ana yinsa har shekaru 10. A lokacin da ake gudanar da binciken, mutane 1057 sun kamu da cutar shanyewar jiki, kuma mutane 327 daga cikinsu sun mutu. Ta takardun tambayoyi, kungiyar nazari ta san cewa, ko wadannan mutanen da aka gudanar da binciken gare su suka samu kulawa daga 'yan iyali da abokai don kwantar da hankulansu ko a'a.

Sakamakon binciken ya bayyana cewa, game da mutanen da ba su samu kulawa sosai daga 'yan iyali da kuma abokai ba, muddin sun kamu da cutar shanyewar jiki, to yiyuwar mutuwarsu ta ninka sau 1.5 in an kwatanta da wadanda suka samu kulawa sosai daga 'yan iyali da abokai. Haka kuma game da mazan da ke cikin binciken, wannan jimla ta kai 1.6, yayin da wannan jimla ta kai 1.3 ga matan da ke cikin binciken.

Wani kwararre a fannin ilmin kiwon lafiyar jima'a ta jami'ar Osaka ta kasar Japan ya bayyana cewa, 'yan iyali da abokai suna iya tallafa wa mutanen da suka kamu da cutar shanyewar jiki wajen tsayawa tsayin daka kan shan magunguna da kuma cin abincin da ke kunshe da gishiri kadan, watakila wannan ya rage yiyuwar mutuwarsu.

Bisa labarin da jaridar Daily Telegraph ta kasar Birtaniya ta bayar, an ce, manazarta na jami'ar Minnesota ta kasar Amurka sun gudanar da bincike ga mutane 4435 da shekarunsu ya kai 30 zuwa 75 da haihuwa, kuma rabinsu suna kiwon kyanwa a gida. Daga baya kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, mutane masu kiwon kyanwa da yawansu ya kai 3.4 cikin dari sun mutu sakamakon barkewar cututtukan zuciya ba zato ba tsammani, amma wannan jimla ta kai kashi 5.8 cikin dari game da wadanda ba su yi kiwon kyanwa ba.

Bayan da suka yi la'akari da dalilan sanya cututtukan zuciya kamar hauhawar jini da shan taba da kuma cutar sukari, manazarta sun yi hasashen cewa, game da mutanen da ba su kiwata kyanwa ba, yiyuwar kamuwa da cututtukan zuciya da shanyewar jini ta karu da kashi 40 cikin dari in an kwatanta da wadanda suke kiwon kyanwa.

Furofesa Adnan Qureshi da ya kula da binciken ya bayyana cewa, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da kiwon kyanwa zai ba da taimako wajen rage matsin lamba da mutane ke samu, da kuma sassauta damuwarsu, ta haka za a iya rage hadarin kamuwa da cututtukan zuciya.