A cikin shirinmu na yau, za mu yi bayani kan ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya na kasar Sin. Game da ranar bikin yanayin sararin samaniya, an bayyana cewa, bisa sauyawar yanayin sararin samaniya da yawan ruwan sama da ake samu da tsawon lokacin saukar jaura da dai sauran almomin halittu ne, aka raba shekara guda don ta zama da matakan lokutan bayyana al'amomin yanayin sararin samaniya lokaci lokaci. Ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya su ne ranakun somawar wadannan matakan lokutan bayyana al'amomin yanayin sararin samaniya. Tsara tsarin ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya shi ne sakamakon da jama'ar zamani aru aru na kasar Sin suka samu a lokacin da suke duddubawa tare da yin nazari kan ilmin yanayin sararin samaniya . Wannan yana da tasiri mai muhimmanci sosai ga harkokin noma. Bisa bayanan da aka tanada, an rubuta cewa, a shekarar 104 kafin bayyanuwar Annabi Isa (A.S), mutanen kasar Sin sun riga sun tsara tsarin ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya, don tunawa da su sosai, mutanen zamanin da sun kuma tsara wakoki dangane da ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya.
Bikin somawar yanayin zafi wato bikin "Lixia" ya kan soma daga ranar 5 ko 6 ko 7 ga watan Mayu a kowace shekara. Bikin somawar yanayin zafi wato "Lixia" na shekarar da muke ciki ya zo ne a ranar 5 ga watan Mayu . A da, mun taba gabatar da cewa, ma'anar kalmar "Li" cikin Sinanci ita ce, soma ke nan, ma'anar "Lixia" ta bayyana cewa, yanayin bazara ya riga ya wuce, daga nan sai a shiga yanayin zafi, kuma yanayin sararin samaniya ya kara zafi sosai, sa'anan kuma ana ruwa da yawa tare da tsawar cida, an duba hasken rana a ranar somawar yanayin zafi don kimanta ko za a sami girbi mai armashi ko girbi maras armashi a wannan shekara. Da akwai karin magana da ke cewa, in ba a yi ruwa a ranar yanayin somawar zafi ba , to za a yi fari har zuwa lokacin da aka soma girbin alkama. Ana kuma cewa, in ba a yi ruwan sama a ranar yanayin somawar zafi ba, to za a rataya kayan noma a sama. Wato ana ganin cewa, abu mafi kyau shi ne ya kasance ana ruwa a ranar bikin yanayin somawar zafi. A hakika dai , da yake akwai bambancin da ke tsakanin kudancin kasar Sin da arewacinta, shi ya sa a kudancin kasar Sin, lokacin zuwa bikin somawar yanayin zafi ya yi daidai da lokacin somawar yanayin zafi, ana soma girbar ganyayyen man tukunya a wurare da yawa , to ya kamata a yi rigakafin maganin ruwan sama. Amma a tsakiyar kasar Sin da arewacinta, ana kasancewa cikin lokacin kawo karshen yanayin bazara, kafin ranar bikin somawar yanayin zafi da bayanta, yanayin sararin samaniya ya kara zafi da saurin gaske, sa'anan kuma iska tana bugawaa bushe, saboda haka an kawo mugun tasiri ga girman tsire-tsiren gonaki, musamman ma a lokacin da alkama ta kusanci lokacin nuna, tana bukatar ruwa da yawa, shi ya sa abu mafi kyau shi ne ana ruwan sama a lokacin. Amma in ba a sami ruwan sama da yawa ba, to ya kamata a yi ban ruwa ga gonakin da aka shuka alkama. Bayan ranar bikin somawar yanayin zafi da bayanta, ana kara samun ciyayi a gonaki, da akwai karin magana da ke cewa, in ba a cire ciyayi a wata rana ba, to bayan kwanaki uku, ba za a iya cire su ba. A lokacin, in ana cire ciyayi, to zafin kasa zai dagu, wannan na da muhimmanci ga kara girman auduga da masara da dawa da gyada da sauransu.
Wajen al'adun gargajiya na kasar Sin, bikin somawar yanayin zafi wato "Lixia" shi ne bikin jama'a. A wani wurin da ke arewacin kasar Sin, har wa yau dai ana bin al'adar cin kwan kaji da aka dafa su cikin ruwa kawai, kowa ya ci, sa'anan kuma fatar mutum za ta yi walkiya sosai tare da lafiya sosai, ba za ta fito da kurji ba. A kudancin kasar Sin, a ranar bikin somawawar yanayin zafi, ana shan sabbin 'ya'yan itatuwa, amma a lardin Fujian da Taiwan da sauran wurare, a kan ci jataulande, domin an ce, in ana cin jataulande, to za a iya samun lafiya a duk lokacin yanayin zafi.(Halima)
|