Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-11 17:19:55    
An fara mika wutar wasannin Olympic na Beijing a gundumar Shagrila

cri

A ran 11 ga wata da misalin karfe 9 na safe ne aka fara mika wutar wasannin Olympic na Beijing a gundumar Shagrila ta yankin Diqing mai cin gashin kansa na kabilar Tibet na lardin Yunnan.

Mutane masu dinbin yawa sun tattara a cibiyar motsa jiki ta kabilun gundumar Shagrila, sanye da tufafi masu kyau, sun yi rawa da rera waka don maraba da zuwan wutar wasannin Olympic. A yayin da aka fara bikin mika wutar, dukkan mutane sun nuna ta'aziyya ga mutanen da suka rasa rayukansu a bala'in girgizar kasa na gundumar Wenchuan har minti daya.

A karfe 9 da minti 15 na safe, an mika wutar zuwa Ma Bajin wato mai mika wutar na farko, daga nan ne, an fara mika wutar wasannin Olympic a gundumar Shagrila.(Lami)