A hakika dai, a gun gasar wasannin Olympic da aka shirya a Athens a shekarar 1896, wasa mafi jawo hankulan 'yan kallo shi ne wasan gudun dogon zango wato Marathon.
Kafin a shirya zama ta farko ta gasar wasannin Olympic ta zamanin yanzu, wani mai ilmin harsuna na kasar Faransa Michel Breal ya taba zuwa kasar Greece domin rangadin aiki, kuma ya nuna girmamawa sosai ga jarumin yakin Marathon Pheidi Pides. A shekarar 490 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihissalam, sojojin Greece sun lashe sojojin Persia a Marathon, soja mai aikawa da umurni Pheidi Pides yana son sanar da albishirin ga sojojin dake zaune a Athens cikin lokaci, sai ya gudu daga Marathon zuwa Athens, har ya gaji sosai, da ya isa, sai ya ce: "Mun ci nasara!" Daga baya kuma ya fadi a kasa.
Labarin ya sa hankalin Breal ya tashi, sai ya rubuta wata wasika ga 'dan uwansa wato babban sakataren kwamitin wasannin Olympic na duniya Coubertin na wancen lokaci inda ya ba da shawara cewa, kamata ya yi a kara wasan dogon zango wato Marathon don tunawa da Pheidi Pides. An tsai da cewa, tsawon gudun Marathon ya yi daidai da tsawon hanya tsakanin Marathon da Athens inda Pheidi Pides ya taba gudu, wato ya kai fiye da kilomita 40. Jama'ar Greece sun mai da hankali sosai kan wasan.
A wancen lokaci, gaba daya a Athens, akwai mutane dubu 130 ne kawai, amma yawan mutane wadanda suke kallon wasan ya kai dubu 100. Wannan a karo na farko ne da aka fara gudun Marathon a kan dandalin wasannin duniya. 'Yan wasa ba su taba shiga irin wannan wasa ba, shi ya sa yawancinsu ba su iya isa wurin karshe na gasar ba, sai sun fadi a kasa. A karshe dai, 'dan wasa daga Greece Spiridon Louis ya samu zama ta farko, sana'arsa ita ce mai jigilar ruwa a kauye.
Da zarar Louis ya isa wurin karshe, sai 'yan kallo suka yi ihu sun dauke shi kuma sun jefa shi zuwa sama. Wani mamban iyalin daular Greece ya ba shi wani cek mai kudi da yawan gaske; wani manajan otel ya samar masa abinci da dakuna a ko da yaushe kuma ba tare da biyan kudi ba; wani manajan kantin aski ya yi masa alkawarin aske gashinsa ba tare da biyan kudi ba; sauran mutane kuwa sun nemi gwamnatin kasar da ta nada Louis da ya zama ministan kasar. A takaice dai, Louis ya zama jarumin al'umma na duk kasar Greece.(Jamila Zhou)
|