Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-11 07:41:07    
Sakamakon da aka samu a gun gasar wasannin Olympic ta birnin Mexico

cri

A shekarar 1968, an shirya zama na 19 na gasar wasannin Olympic a birnin Mexico wanda tsayinsa ya fi lebur teku da mita 2240, daga nan kasar Mexico ta zama kasa ta farko wadda ta samu iznin shirya gasar wasannin Olympic a Latin Amurka, saboda haka, gwamnatin kasar Mexico tana mai da hankali sosai kan wannan. Shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasar Mexico na yanzu Felipe Munoz Kapamas ya waiwaya cewa, yayin da wata kasa ta samu iznin shirya gasar wasannin Olympic, sai dukkan jama'arta sun yi kwazo da himma kan aikin share fage domin nuna wa jama'ar kasashen duniya namijin kokarin da suka yi, a sanadiyar haka, an kago tsarin musamman na Mexico a gun zama na 19 na gasar wasannin Olympic a shekarar 1968. Ya ce:  "Birnin Mexico ya samu cikakkiyar nasarar shirya gasar wasannin Olympic, haka ya canja ra'ayin kuskuren da mutanen kasashen waje da yawa suka dauka kan kasar, 'yan kasar Mexico sun gamsu da sakamakon sosai da sosai. Dalilin da ya sa haka shi ne domin kasar Mexico ta shaida wa jama'ar kasashen duniya karfinta ta hanyar shirya gasar wasannin Olympic cikin nasara. Alal misali, a karo na farko ne muka soma yin amfani da na'urar lantarki wajen kididdigar lokacin gasa."

A ran 12 ga watan Oktoba na shekarar 1968, an bude gasar wasannin Olympic a birnin Mexico, kungiyoyin wakilan da suka zo daga kasashe da shiyyoyi 112 sun halarci wannan gasa. A gun bikin bude gasar, Enriqueta Basilio, 'yar wasan guje-guje da tsalle-tsalle daga kasar Mexico wadda shekarunta na haihuwa suka kai 20 kawai ta kunna babbar hasumiyar wutar yula, da haka ta zama mace ta farko wadda ta kunna wutar yula a tarihin wasannin Olympic. Babban direktan zartaswa na kwamitin wasannin Olympic na yanzu kuma babban alkalin wasa na gasar kwallon raga a gun gasar wasannin Olympic ta Mexico ta shekarar 1968 Eduardo Gorraez Larrinaga ya waiwaya cewa,  "'Yar wasa daga Mexico ta kunna babbar hasumiyar wutar yula a filin wasannin Olympic na birnin Mexico, ta zama mace ta farko wadda ta kunna wutar yula a tarihin wasannin Olympic."

Ban da wannan kuma, a gun gasar wasannin Olympic ta birnin Mexico, an kago abubuwa da yawa. Eduardo Gorraez Larrinaga ya ci gaba da cewa,  "A gun gasar wasannin Olympic ta birnin Mexico ta shekarar 1968, a karo na farko ne an soma yin amfani da fasahar telebiji mai launi don watsa labaran gasanni kai tsaye, kuma a karo na farko ne an kafa cibiyar watsa labarai musamman domin 'yan jaridu saboda suna samun sakamakon gasanni kai tsaye da kuma cikin lokaci."

Kazalika, 'yan wasa da suka zo daga wurare daban daban sun samu sakamako mai gamsarwa, alal misali, 'dan wasan dogon tsalle daga kasar Amurka Bob Beamon ya kago sabon matsayin bajimta na duniya da mita 8.9 kuma ya rike da matsayin da shekaru 23. Abun da ya fi burge mu shi ne 'yan wasa daga kasashen Afirka sun samu dukkan zakarun gasannin gudun dogon zango wato daga wasan gudun mita 1500 zuwa gudun marathon. Wannan ya alamanta cewa, wasan gudun dogon zango na Afrika ya samu ci gaba cikin sauri.

Game da sakamakon da aka samu a gun gasar wasannin Olympic ta birnin Mexico, shugaban kungiyar wakilai ta kasar Mexico na wancen lokaci Carlos Padilla Becerra ya ce:  "Gasar wasannin Olympic da aka shirya a birnin Mexico kafin shekaru 40 da suka shige ta ba mu babban mamaki, kafin wannan, mutane da yawa sun nuna shakka kan karfinmu, lallai mun gamsu da sakamakon da muka samu kwarai da gaske." (Jamila Zhou)