Ran 10 ga wata, bisa urmunin da babban ofishin ba da jagoranci ga ayyukan fama da bala'in girgizar kasa da ayyukan ceto na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar, ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gabatar da cewa, ya zuwa ran 10 ga wata da tsakar rana da misalin karfe 12, mutane 69146 ne suka rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa ta Wenchuan ta lardin Sichuan, yayin da wasu fiye da dubu 370 suka jikkata, sa'an nan kuma, wasu 17516 sun bace.
Bisa rahoton da ma'aikatar harkokin jama'a ta kasar Sin ta bayar, an ce, ya zuwa ran 10 ga wata da tsakar rana da misalin karfe 12, kasar Sin ta karbi kayayyakin taimako da kuma kudaden tallafi fiye da kudin Sin yuan biliyan 44.4 daga rukunoni daban daban na zaman al'ummar kasa na gida da na waje, ta kuma kebe kudin Sin yuan biliyan 13.7 ko fiye zuwa wuraren da ke fama da bala'in.
Kazalika kuma, ma'aikatar kudi ta kasar Sin ta ba da rahoto da cewa, ya zuwa ran 10 ga wata da tsakar rana da misalin karfe 12, hukumomi na matakai daban daban sun zuba kudin Sin yuan fiye da biliyan 23.4 domin fama da bala'in girgizar kasa da kuma ayyukan ceto.(Tasallah)
|