Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-10 16:07:04    
An gama aikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a birnin Lijiang

cri

An gama aikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a yau 10 ga wata da safe a birnin Lijiang dake kudu maso yammacin kasar Sin.

Yau da misali karfe 8 da safe, an yi bikin fara mika wutar a filin jama'ar birnin Lijiang. Kafin bikin, dukkan mahalartan bikin sun nuna ta'aziyya ga mutanen da suka rasa rayukansu a girgizar kasa ta lardin Sichuan har minti daya. Sa'an nan, wata yariya ta kabilar Qiang mai suna Zhang Zilan da ta fito daga yankin dake fama da bala'in girgizar kasa na gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, da wani yaro na kabilar Naxi mai suna He Zhensheng wanda aka haifi shi a ran 3 ga watan Fabrairu na shekarar 1996 da aka samun bala'in girgizar kasa a birnin Lijiang, sun daga wutar yola ta 'Xiangyun' tare, kuma sun gama aikin mika wutar yola na zango na farko.

Daga bisani kuma, an kai wutar yola zuwa babban titin Xianggelila da lambun shan iska na kayayyakin gado na duniya da sauran shahararrun wurare, bayan da aka mika wutar a kan hanyar da tsawonta ya kai kilomita 8.9, mai mika wutar ta karshe Madam Yang Yiben ta cinna wutar kwanon wuta dake Ganhaizi.

Masu mika wutar 208 sun shiga cikin aikin mika wutar yola a birnin Lijiang, ciki har da 101 na kanannan kabilu 14.(Lami)