Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-09 21:18:26    
Wen Jiabao ya shugabanci taro domin nazari kan ci gaba da gudanar da ayyukan jiyya da rigakafin annoba a yankunan da ke fama da girgizar kasa

cri

A ran 9 ga wata, Wen Jiabao, memban zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS kuma firayim ministan kasar Sin kuma babban mai ba da umurni kan fama da girgirzar kasa da ceton mutane ya shugabanci taro domin nazari kan ci gaba da gudanar da ayyukan jiyya da rigakafin annoba a yankunan da ke fama da bala'in kamar yadda ya kamata, da kuma ayyukan fama da girgizar kasa da ceton mutane a lardunan Gansu da Shanxi.

Taron ya nuna cewa, yanzu ana gudanar da ayyukan rigakafin annoba daga dukkan fannoni kamar yadda ya kamata, ba a samo cututtuka masu yaduwa da al'amuran kiwon lafiyar jama'a na ba zata ba a yankunan da ke fama da bala'in. Yanzu ya kamata a dora muhimmanci kan ceton mutanen da suka ji raunuka masu tsanani domin yin iyakacin kokari wajen rage yawan mutuwar mutanen da suka ji raunuka masu tsanani da kuma yawan mutanen da suka nakasa. Haka kuma ya kamata a gudanar da ayyukan kiwon lafiya da rigakafin annoba yadda ya kamata, da inganta ayyukan daidaita muhallin kiwon lafiya na yankunan, da kuma gudanar da ayyukan shawo kan annoba bayan da ruwan tafkin da ya samo asali daga girgizar kasa ya malala. Ban da wannan kuma ya kamata a mayar da odar ayyukan ba da hidima kan jiyya da kiwon lafiya na yankunan tun da wuri domin tabbatar da biyan bukatun fararen hula a wannan fanni.(Kande Gao)