Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-09 20:44:18    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- A ran 19 ga wata da yamma da misalin karfe 2 da minti 28, an ji karar jiniya da ta motoci da jiragen kasa a birnin Lhasa, hedkwatar jihar Tibet mai cin gashin kai ta kasar Sin, dubban jama'a 'yan kabilu daban-daban wadanda suka je babban filin fadar Potala tun tuni sun yi tsit tare domin nuna alhini ga wadanda suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasar da ta faru a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan.

Bayan da aka yi bikin nuna alhini, kuma mutane da yawa suna tsaye cik har dogon lokaci, ba su son tashi daga can. Ko ina ana iya ganin fararen hula suna yin sujada da huduba a gaban fadar Potala.

Daga karfe 2 da minti 31 na wannan rana da yamma, sufaye na dakin ibadan Jokhan sun fara yin addu'a , sufaye fiye da 90 wadanda ke sanye da manyan riguna masu launin ja suna yin huduba da murya daya cikin wani babban dakin yin addu'a, sun yi haka ne domin yin addu'a ga wadanda da suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasar da ta faru a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, da yin fatan alheri ga mutanen da suke da rai.

Bayan aukuwar babbar girgizar kasa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, mutane 'yan kabilu daban-daban na jihar Tibet sun sha yin bukukuwan ba da kyautar kudi da samun karo-karon kudin da aka bayar domin nuna kauna ga mutane masu fama da bala'in girgizar kasa.

---- Bisa ci gaban da aka samu wajen yawan kayayyakin tarihi da aka tono daga karkashin kasa, kayayyakin tarihi na tsohon mazaunin Loulan da aka binne su karkashin rairayi suna ta kara jawo hankulan mutane. Domin kiyaye kayayyakin tarihi masu daraja da aka tono, da gwada al'adu masu halayen musamman a yammacin kasar Sin, ana sa rai cewa za a fara aikin gina wani babban dakin ajiye kayayyakin tarihi na Loulan daga karshen rabin shekarar da muke ciki, fadin kasar da aka kebe domin gina wannan babban dakin kuma ya kai kusan murabba'in mita dubu 70.

Bisa labarin da gwamnatin jama'ar ta gundumar Ruoqiang ta jihar Xinjiang ta kasar Sin ta bayar an ce, fadin gini na babban dakin ajiye kayayyakin tarihi na Loulan wanda ake kokarin tsara fasalin ginawa ya kai murabba'in mita 3200, wannan babban dakin za a gina shi ne bisa tsarin ginin gargajiya irin na Loulan na tsohon zamani, kuma za a yi sakakkun kayayyki da na mutun-mutumin budda na lokutan daban-daban a bangwayen waje na babban dakin, a cikin kuma za a gina dakunan nune-nunen kayayyakin dake hade da kayayyakin tarihi da na dabbobi da tsire-tsire, da kuma dakin nuna albarkatun ma'adinai.