Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-09 20:42:22    
An sami sabon ci gaba wajen bunkasa tattalin arzikin garin Datang na kasar Sin ta hanyar kirkirawa

cri

Gari mai suna Datang wani karamin gari ne na jihar Zhejiang da ke a gabashin kasar Sin. Ya shahara sosai wajen sakar safar kafa a kasar Sin. Yawan takin safar kafa da yake samar ya kan kai biliyan 8 a ko wace shekara, wato ke nan ya dauki kashi 30 cikin dari bisa jimlar takin safar kafa da ake samar a dukan duniya.

Aikin sakar safar kafa babbar sana'a ce ga garin Datang da kauyuka 12 da ke kewayensa. Yawan ma'aikatan da ke aiki a masana'antun sakar safar kafa ya wuce dubu 100. Bisa kidayar da aka yi, an ce, yawan na'urorin sakar safar kafa ya riga ya kai dubu 100 a wannan gari da kauyukansa a shekarar 2006, yawan takin safar kafa da suke fitarwa ya wuce biliyan 11.8, jimlar kudin da suke samu daga wajen safar kafa ya kai kimanin kudin Sin Yuan biliyan 28. Amma duk da haka mutanen garin ba su gamsar da sakamakon da suka samu ba, sun fara zura ido ga kasuwannin duniya.

Hukumar garin ta ba masana'antun kwarin gwiwa don samar da shahararrun samfurorin safar kafa a duniya ta hanyar kirkirawa. Kamfani mai suna Danjiya yana daya daga cikin kamfanonin sakar safar kafa da suka zuba makudan kudade wajen binciken kimiya tun can da. Malam Zhu Tianyong, jami'in wannan kamfanin ya bayyana cewa, "kamfaninmu yana hadin kansa da Jami'ar Donghua da Kolejin koyon aikin injiniya ta lardin Zhejiang. Ya zuwa yanzu, mun riga mun sami sakamako wajen binciken kimiyya da fasaha a fannoni uku. Daya daga cikinsu ya sami lambar yabo daga wajen gwamnatin kasar Sin da ta jihar Zhejiang. Sabbin ire-iren safar kafar da aka saka ta hanyar yin amfani da sakamakon nan sun kasance cikin sahun gaba a kasar Sin da kuma duniya."

Babban kamfanin yin zaren Spandex a Turanci da ake kira Huahai yana daya daga cikin manyan kamfanoni na zamani biyu a garin Datang. Malam Du Chunshu, mataimakin babban manajan wannan kamfani ya bayyana cewa, zaren Spandex wani irin zaren zamani ne mai inganci sosai. Kamfaninsa ya shafe shekaru da yawa yana kokari sosai wajen yin bincike kan irin wannan zare mai inganci. Ya kara da cewa, "kamfaninmu ya kafa wata cibiyar nazarin kimiyya. Bisa bukatun da ake yi a kasuwanni daban daban, kamfaninmu ya kan yi amfani da kayayyakin gwaje-gwajensa wajen fitar da sabbin takin safar kafa iri daban daban don biyan bukatun da ake yi a kasuwanni. Ban da wadannan kamfanoni biyu, kuma akwai kamfanoni da yawa a garin Datang wadanda ke kokari sosai wajen binciken kimiyya don samar da sabbin ire-iren safar kafa ta hanyar kirkirawa."

Malam Guo Jianbo, magajin gari na Datang ya bayyana cewa, "yayin da ake bunkasa wata sana'a, wajibi ne, a daidaita batun binciken kimiyya da kyau. In ba haka ba, karin ribar kudin da ake samu daga kayayyakin da ake fitarwa ba zai yi yawa ba, sa'an nan tsawon ran kayayyakin ma ba zai dade ba."

Yanzu, garin Datang ya riga ya kafa wani cikakken tsarin kirkirawa ta hanyar kimiyya da fasaha domin sana'ar sakar safar kafa. Kuma ta hanyar kirkirawa, an sake ciyar da garin Datang gaba, sa'an nan samfurorin safar kafa na garin Datang kullum sai kara shahara suke yi a kasuwannin kasa da kasa. (Halilu)