Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-09 20:02:36    
Ana sa ran cewa, kasar Sin za ta yi girbin hatsi mai armashi a lokacin zafi a shekaru 5 a jere

cri

Adadin da ma'aikatar aikin gona ta kasar Sin ta samu ya nuna cewa, a shekarar da muke ciki, ana sa ran cewa, kasar Sin za ta yi girbin hatsi mai armashi a lokacin zafi, haka kuma za ta sami karin hatsi a shekaru 5 a jere. Kwararru masu ilmin hatsi sun nuna cewa, yanzu kasar Sin tana ajiye isasshen hatsi, tana iya samar wa kanta da isasshen abinci, tana kuma ba da gudummowa mai yakini wajen tabbatar da kwanciyar hankali a kasuwannin hatsi na duniya.

A lokacin zafi, kasar Sin ta fi samun girbin alkama, wadda aka fi samunta a lardin Henan da ke yankin tsakiyar kasar Sin. Wei Zhongsheng, babban mai nazarin harkokin tattalin arziki na hukumar aikin gona ta lardin Henan ya bayyana cewa, ana sa ran cewa, yawan hatsin da Henan za ta samu a lokacin zafi na wannan shekara zai karya adadin da aka samu a tarihi. Ya ce,'Saboda an fadada gonakin shuka hatsi da kara ire-iren hatsi da kuma kyautata ingancin hatsi a wannan shekara, shi ya sa an kiyasta cewa, yawan hatsin da za a samu a wannan lokacin zafi zai kai misalin kilo biliyan 30.5, wanda ya karu fiye da kilo miliyan 750 bisa na makamancin lokaci na shekarar bara. Ma iya cewa, jimlar hatsin da Henan za ta samu a wannan lokacin zafi za ta kai sabon matsayi a tarihi. Saboda ana ci gaba da inganta karfin manoma da ba su gatanci ta fuskar manufa, haka kuma, ana ta kyautata matsayin fasahohin aikin gona, manoma kuwa suna ta kara kuzarinsu na shuka hatsi, shi ya sa Henan tana da boyayyen karfi wajen samar da karin hatsi.'

Ko da yake a farkon rabin wannan shekara, kasar Sin ta taba shan wahalar bala'u daga indallahi, amma Yin Changbin, wani kwararre mai ilmin hatsi da ke aiki a cibiyar nazarin kimiyyar aikin gona ta kasar Sin, ya bayyana cewa, bala'u daga indallahi sun kawo wa kasar Sin illa kadan wajen samar da hatsi, haka kuma ba su hana kasar Sin ta sami isasshen abinci ba. Ya ce,'A farkon wannan shekara, an gamu da bala'in dusar kankara a wasu wuraren kasar Sin, amma dusar kankara ta taimaka wa hatsi da su girma. Ban da wannan kuma, an yi girgizar kasa a lardin Sichuan, wasu wuraren da suka fi fama da bala'in suna kasancewa a cikin manyan tsaunuka, inda ba su sayar da hatsi da yawa ba. Shi ya sa ko da yake yawan hatsin da za a samu a wadannan wuraren da ke fama da bala'in zai ragu da kashi 10 cikin dari, amma ba zai kawo illa ga kasar Sin da ta sami isasshen abinci ba.'

A shekarun baya, yawan hatsin da kasar Sin ta samu na ta karuwa ba tare da tangarda ba, kasar Sin tana da isassun muhimman amfanin gona, haka kuma, a galibi dai, yawan hatsin da ake kai su a kasuwa ya fi wanda ake bukata. Mr. Yin ya kara da cewa, dukkansu kyakkyawan sakamako ne da aka samu domin kasar Sin ta dauki manufofin mara wa manoma baya da kuma ba su gatanci a shekarun nan da suka wuce, ta haka an karfafa gwiwar manoma da su shuka hatsi. Yanzu kasar Sin tana ajiye hatsi da yawa, ba ta gamu da matsalar karancin abinci ba.

A kwanan baya, a lokacin da yake halartar taron duniya a tsakanin manyan jami'ai kan samun isasshen abinci a birnin Rome, Sun Zhengcai, ministan aikin gona na kasar Sin ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta ba da muhimmiyar gudummowa wajen samar da isasshen abinci a duniya. Sa'an nan kuma, ya ci gaba da cewa,'Kasar Sin ta dogara da kanta, ta sami nasarar samar wa mutanenta biliyan 1 da miliyan 300 isasshen abinci, wannan ya kasance muhimmiyar gudummowa ce wajen tabbatar da samun isasshen abinci a duniya. Kasar Sin tana raya cinikin shigi da ficin hatsi yadda ya kamata, kuma tana sayar da hatsi zuwa ketare a maimakon shigo da su. Bugu da kari kuma, kasar Sin ta yi iyakacin kokari domin ba da abubuwan kyauta ga hukumar FAO ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ba da abincin taimako ga wasu kasashen da ke karancin abinci, ta kuma taimaka wa kasashe masu tasowa a fannonin fasaha da horar da kwararru.'(Tasallah)