Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-06 16:46:41    
Jami'o'i sun tsara wani shirin musamman domin daukar daliban da za su shiga jarrabawar neman shiga cikin jami'a dake yankunan da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su

cri

Za'a yi jarrabawar gama-gari ta neman shiga cikin jami'a a nan kasar Sin daga gobe ranar 7 ga wata har zuwa jibi ranar 8 ga wata. Domin bada tabbaci ga daliban da za su shiga jarrabawar a yankunan dake fama da bala'in girgizar kasa wajen samun zarafin shiga cikin jami'a daidai wa daida, ma'aikatar ilimi ta kasar Sin ta riga ta bukaci jami'o'i daban-daban da su tsara shiri na musamman domin daukar dalibai.

Daliban da mummunan bala'in girgizar kasa ya shafa na kushe da daliban da za su shiga cikin jarrabawar neman shiga cikin jami'a da yawansu ya kai kimanin dubu 120 a gundumomi guda 57 dake lardunan Sichuan da Gansu da dai sauransu. A halin yanzu, jami'o'i daban-daban sun riga sun sake daidaita shirin daukar dalibai, yawan daliban da za su more daga wannan shirin musamman ya dau akalla kashi 20 daga cikin dari na dukkan daliban da za'a dauka a lardin Sichuan, haka kuma, yawan daliban da za su more daga wannan shirin musamman ya dauki akalla kashi 10 daga cikin dari na dukkan daliban da za'a dauka a lardin Gansu. Dukkansu sun dara yawan daliban dake yankunan dake fama da bala'in girgizar kasa na jimlar yawan daliban da za su shiga jarrabawar a wadannan larduna biyu.(Murtala)