Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-06 15:37:49    
An fara mika wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing ta rana ta farko
a lardin Guangxi

cri

Yau ran 6 ga wata da safe, an cimma nasarar mika wutar yola ta gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beiking a rana ta farko a lardin Guangxi.

Birnin da aka yi bikin mika wutar a rana ta farko shi ne shahararren birnin yawon shakatawa na kasar Sin Guilin, mai dauke da wuta na farko shi ne zakarar wasannin daukan nauyi a gun gasar wasannin Olympic na shekarar 1996 Tang Lingsheng, kuma mutumin da ya sami lambar yabo ta tagulla a gasar wasannin Olympic na shekarar 1992 Xiao Jiangang zai zama wanda zai dauki wutar na karshe. Tsawon hanyar mika wutar wasannin Olympic na Beijing a birnin Guilin zai kai kilomita 15, kuma za a bi ni'imtattun wurare da dama kamarsu wurin yawon shakatawa na Qixing da tekun Lijiang da dutsen Xiangbi.

A gun bikin fara yin yawo, dukkan ma'aikata da za su shiga cikin bikin, sun yi shiru kuma sun nuna alhini ga mutanen da suka rasu a gun girgizar kasa da ta fadawa gundumar Wenchuan har minti daya, masu dauke da wuta da masu sana'o'i daban daban na birnin Guilin sun shiga cikin bikin ba da kudin gudummawa ga yankunan da bala'in girgizar kasa da ya shafa.(Bako)