Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-06 11:24:19    
Mr. Wen Jiabao ya yi rangadin ayyukan fama da tafki mai shinge da ke Tangjiashan

cri

Ran 5 ga wata, Mr. Wen Jiabao firaministan kasar Sin ya je lardin Sichuan domin sake yin rangadin ayyukan fama da tafki mai shinge da ke Tangjiashan wanda ke barzana ga zaman lafiyar muliyan mutane. Ya jaddada cewa, yayin da ake tinkarar tafki mai shinge, dole ne a kare ko wane mutum.

Kafin kwanaki 13, Mr. Wen Jiabao ya taba kai ziyara ga halin da wannan tafki mai shinge ke ciki, kuma ya rarraba ayyukun kawar da hadari nan take. A cikin kwanakin baya, mutame masu aikin inginiya suna ta kokari sun yashe wata hanyar ruwa da tsawonta ya kai mita 400 domin kawar da hadarin ambaliya. Ban da haka kuma, an rigaya an kwashe jama'a da yawansu ya kai dubu 200 zuwa wurare masu kwanciyar hankali.

Mr. Wen Jiabao ya yi nuni da cewa, bayan aukuwar bala'in matsanancin girgizar kasa, hadarurrukan da girgizar kasa ta hassasa suna barazana zaman lafiyar jama'a. Dole ne a kawar da hadarin tafki mai shinge da sauri, da kuma karfafa tsarin sa ido da yin gargadi, da kuma cigaba kyautata shirin kawar da hadari ta hanyar inginiya da shirin kwashe jama'a zuwa wurare masu kwanciyar hankali.